Fitattun 'Yan Arewa 100 A Shekarar 2016

Daga HAYATU [ANGALADIMA Da SHARFADDEEN SIDI Tare Da Rahotannin Wakilanmu

Jerin mutanen da ke tafe 'Yan asalin yakin Arewacin Nijeriya ne da suka yi fice a shekarar 2016 ta fannoni daban-daban da suka ha]a da fagen mulki da siyasa da tattalin arziki da sarauta da kimiyya da fasaha da ilimi da bun}asa addini da wayar da kan jama'a da ilmantarwa da fa]akarwa da bayar da nisha]i da sauran fannonin da suka sanya yankin Arewa ya ]aukaka tare da yun}urin cimma tsararrakinsa. Wasu daga cikinsu sunansu bai yi amo sosai ba, amma kuma rawar da suka taka gagarumace da tarihi ba zai manta da su ba.

1. Shugaban {asa Duk da sa~anin ra’ayoyin jama’a musamman tsakanin magoya bayansa da masu }orafi da salon tafiyar gwamnatinsa a tsawon shekara ]aya da rabi da soma mulkinsa, Shugaba Muhammadu Buhari na ci gaba da kasancewa wani gwarzon namijin duniya da har zuwa wannan lokaci mafi yawan al’umma ke ci gaba da nuna goyon bayansu zuwa gare shi. Wannan ne ya sa shugaban kasancewa a sahun gaba na ‘ya’yan yankin Arewa da suka taka rawar gani kana suka kasance fitilu ko kuma taurarin da suka haska tare da }awata shekarar 2016 da ta shu]e. Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya kar~i ragamar shugabancin Nijeriya a daidai wani lokaci da zai fi sau}in kwatantawa da na rashin tabbas da }a}a-nika-yi, inda kusan komai na }asar yake a tagayyare, ya samu nasarar dasa tsiron tabbas a zukata da yawa wa]anda a baya rashin tabbas da kuma kokwanto suka yi katutu a cikinsu. A cikin wannan zango na }asa da shekara biyu da somawar mulkinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar mayar da Nijeriya akan tafarkin da ya kamace ta na }asaitacciyar }asa tare da dawo mata da martabarta a idon duniya a matsayinta na giwa a tsakanin }asashen Nahiyar Afurka. A cikin wannan ]an }an}anen lokaci Shugaba Buhari ya samu nasarar daidaita sahun fannoni daban-daban da suka ji~inci ci gaban }asar nan. Gwamnatinsa ta samu nasarar gano bakin zaren matsalar tsaro da ta }i ci ta }i cinyewa a }asar, inda yanzu haka rundunar sojin Nijeriya ta kammala karya lagon ayyukan {ungiyar inda tuni dukkan sansanonin {ungiyar da ma shi kansa babban mafakar {ungiyar na }ungurmin Dajin Sambisa suka fa]a hannun rundunar sojin }asar. Su ma }ungiyoyin IPOB na ‘yan awaren haramtacciyar }asar Biafra da takwarorinsu tsagerun yankin Neja-Delta, an samu nasarar da}ile tasirinsu wajen haddasa duk wata tashin-tashina ko kuma barazana irin ta tsaro a }asar nan. Haka ma an soma ganin farar safiya a fannin farfa]owa da tattalin arzikin }asar nan sanadiyar soma samun daidaito a sha’anin samar da hasken lantarki da kuma samun nasarar sake janyo masu saka jari daga waje, wa]anda a baya fargaba ta sanya suke ]ar-]ar da zuba dukiyarsu a harkokin kasuwancin }asar. Ya}ar ayyukan cin hanci da yanzu haka gwamnatin Buhari ta sanya gaba kuwa, al’amari ne da ke shan yabo daga ciki da wajen Nijeriya, an samu nasarar taka birki ga wawurar dukiyar jama’a baya ga ma}udan ku]a]e da aka }wato a hannun gur~atattun mutane da suka yi rub da ciki da dukiyar al’umma. Matakin da gwamnatinsa ta ]auka na bayar da kulawar musamman ga harkokin noma, mataki ne da zai fa’idanci yankin Arewa fiye da duk wani yanki da ke }asar nan kasancewar wannan fanni shi ne }ashin bayan tattalin arzikin fiye da kashi 80 cikin 100 na al’ummar wannan yanki. Tuni ma da aka soma girbar alfanun da ke cikin wannan mataki ganin cewa yanzu haka al’ummar wannan yanki sun tsunduma gadan-gadan cikin harkokin noman rani da na damina a wani ma’auni da ba a ta~a ganin irinsa ba tun bayan shekarun 1970.

2. Sanata Bukola Saraki (Shugaban Majalisar Dattawa ta {asa) Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki na ]aya daga cikin limaman canjin da gwagwarmayar siyasarsu ta haifar da gagarumin sauyi a salon tafiyar siyasar }asar nan. Yana cikin rukunin matasan ‘yan siyasa kuma shugabanni da a yau yankin Arewa ke tin}aho da su, domin yana sahun gaba wajen fa]i-tashin gwagwarmayar neman sauyi da shi da wasu takwarorinsa suka assasa tun daga kan kafa ~angaren aware na sabuwar PDP daga tsohuwar jam’iyyar PDP har zuwa ga shigowarsu jam’iyyar APC. Sanata Bukola Saraki wanda yanzu haka yake wakiltar maza~ar [an Majalisar Dattawa ta Kwara ta Tsakiya tun daga shekarar 2011 har zuwa yau, yana ]aya daga cikin manyan iyayen jam’iyyar APC kuma babban ginshi}inta a Jihar Kwara da ma ]aukacin yankin Arewa ga baki ]aya, ya taka rawar gani ainun a dukkan gwagwarmayar jam’iyyar tun daga kan matakin jiha har zuwa na tarayya. Ga zahiran alamu shi ne ya ]are kujerar halifancin daular siyasar da mahaifinsa, marigayi Abubakar Olusola Saraki ya kafa a lokacin rayuwarsa, ganin irin ]imbin tasirin siyasar da yake da shi yanzu haka. Salon shugabancinsa ga Majalisar Dattawa ta }asa a cikin shekara ]aya da rabi da ma irin yadda ya samu nasarar toshe duk wata kafa da za ta iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin membobin Majalisar da suka fito daga jam’iyyun siyasa masu ra’ayoyi da a}idu masu cin karo da juna, ya sanya shi a cikin hazi}an shugabanni da yankin Arewa ke bugun gaba da su musamman a irin yadda suke }o}arin ba wa mara]a kunya tare da tallata sunan yankin a idon duniya. Shugabancinsa ya taimaka wajen samun nasarar gwamnati mai ci a sassa daban-daban na inganta rayuwar al’umar }asar nan. Wannan ya sanya shi cikin jerin fitattun shugabanni ‘yan asalin yankin Arewa da suka yi fice kana suka haska a shekarar 2016.

3. Honarabul Yakubu Dogara (Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya) Tun daga shekarar 2007 da aka soma za~ensa a matasayin [an Majalisar Tarayya mai wakiltar maza~ar tarayya da ta ha]a }ananan hukumomin Bogoro da Dass da kuma Tafawa |alewa da ke jihar har zuwa za~ensa a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai a watan Yunin shekarar 2015, Honarabul Yakubu Dogara ya fita daban a cikin jerin wakilan jama’a kuma shugaba a cikin matasan ‘yan siyasar da yankin Arewa ke alfahari da su. Yadda za~arsa a matsayin shugaban Majalisar Wakilai ya zo a matsayin ba-zata ga wasu, haka tarin nasarorin da shugabancin nasa ya samar ya kasance abin mamaki a wurinsu. Honarabul Yakubu Dogara gogaggen lauya ne da ya ha]a gogewarsa da }warewa akan al’amuran shugabanci kamar dai yadda a yau ake gani a zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya inda ya ke samun gagarumar nasarar ha]e kan membobin Majalisar a matsayin tsintsiya ma]aurinki ]aya duk da irin rigima da hayagagar shugabanci da sauran yun}urin kai ruwa rana da suka sha neman kunno kai a Majalisar. Ko bayan kasancewarsa akan matsayi na hu]u a tsarin jadawalin shugabannin da ke juya sitiyarin sha’anin mulkin }asar nan, Honarabul Dogara wani babban jigo ne a cikin jigogin siyasa da mulki da wakilci da yankin Arewa ya samar wa]anda a yau yankin da ma }asa baki ]aya ke cin moriyarsu. Rawar da ya taka da kuma wadda yanzu haka yake kan takawa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Tarayya ta kasance abin alfahari kuma abin koyi ga na baya.

4. Kashim Shettima (Gwamnan Jihar Borno) Babu wani Gwamna a tarayyar Nijeriya da gwamnatinsa ta soma mulki a cikin gagarumin }alubale makamancin wanda Shugaban Dandalin Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya samu a lokacin da ya kar~i ragamar mulkin jihar Borno a shekarar 2011. Sai dai wani abin birgewa shi ne, duk da wannan }alubale da ya yi wa jiharsa }awanya, bai yi sanyin gwiwa ba, bai karaya ba, bai kuma razana ba ballantana ya kasa wajen sauke nauyin da jama’arsa suka ]ora masa. Salon tafiyar mulkinsa da kuma nasarorin da yake samu sun tabbatar da hakan. Babu abin musantawa akan cewa tun daga shekarar 2011 da gwamnatinsa ta zo kan mulki har zuwa yau, jiharsa ta Borno ta fuskanci gagarumin na}asu a babban sinadarin ci gaba, wato zaman lafiya, amma kuma duk da haka tarin ci gaban da ya samar a cikin irin wannan yanayi na rashin kwanciyar hankali, ya mayar da shi wani gwarzo da duniya ta jinjinawa a fagen fuskantar }alubale. Wannan jarumtaka na daga cikin abubuwan da takwarorinsa gwamnonin Arewa su 19 suka hango kana bakinsu ya zo ]aya wajen dam}a masa ragamar shugabancin Dandalin Gwamnonin yankin na Arewa. Wannan kurum ya isa ya tabbatar da kasancewarsa gwarzon gwamna ba wai na yankin Arewa ba kurum, har ma a matakin }asa baki ]aya, nasara a cikin }alubale na daga cikin abubuwan da suka sanya tauraruwarsa ta yi wa ta saura fintinkau wajen haskawa a shekarar 2016.

5. Yahaya Bello (Gwamnan Jihar Kogi) A tsawon tarihin mulki da na siyasar jihar Kogi, Gwamna Yahaya Bello ne mutum na farko da ya ta~a mulkin jihar a matsayen za~a~~en gwamnan farar hula daga }abilar Ibira, wannan na daga cikin abubuwan da suka karkato hankulan jama’a a ciki da wajen jihar ta Kogi zuwa kallon rawar da zai taka domin amfani da ita wajen bambancewa tsakanin jiya da yau. Shekara ]aya ta mulkinsa ta taimaka wajen tabbatar da gogewarsa da ma }warewarsa a fagen shugabancin al’umma. Gwamnan ya fitar da matasan ‘yan siyasa kunya, ya fitar da ‘yan }abilarsa ta Ibira kunya, ya kuma fitar da jam’iyyarsu ta APC kunya ta hanyar shimfi]a mulki irin na ciyar da al’umma gaba ba tare da nuna wariya ko bambancin yanki ko }abila ba a fa]in jihar ta Kogi wadda ta }awatu da tarin manya da }ananan }abilu da tafiyar da mulkin da zai gamsar da bu}atunsu ke da matu}ar wuya. Tasirin Gwamna Yahaya Bello a fagen siyasar jihar Kogi ba }arami ba ne, domin ko a za~en fitar da gwanin ]an takarar gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar wanda marigayi Prince Abubakar Audu ya lashe, Alhaji Yahaya Bello ne ke mara masa baya a yawan }uri’u daga cikin ‘yan takara kusan 20 da suka fafata a za~en, wannan ne ma ya sa jam’iyyar ta APC ba ta yi wata-wata ba wajen bayar da sunansa domin maye gurbin marigayi Prince Audu, wanda Allah ya kar~i ransa ana gab da bayyana sakamakon za~en gwamnan jihar da aka gudanar a watan Nuwamban shekarar 2015. Irin yadda Gwamnan ya samar da sabuwar fuska ga Jihar Kogi ya sanya shi kasancewa sahun gaba a sahun shugabannin da suka baiwa mara]a kunya a shekarar 2016.

6. Simon Ba}o Lalong (Gwamnan Jihar Filato) Gwamna Jihar Filato Simon Ba}o Lalong zai iya kasancewa ]aya daga cikin fitattun ‘yan siyasar da suka da]e suna jan zarensu a fagen siyasar }asar nan, gogaggen lauya ne kuma masani akan harkar dokokin }asa. Ya ta~a wakiltar al’ummar maza~ar Shendam a Majalisar Dokoki ta jihar Filato a shekarar 1999, ya ri}e kujerar Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar a shekara ta 2000 har ma ya kafa tarihi a matsayin Shugaban Majalisar jihar mafi da]ewa akan mulki inda ya kwashe shekara bakwai yana jagorancin Majalisar daga shekarar 2000 zuwa 2006. A cikin wannan lokacin ne kuma takwarorinsa shugabannin majalisun dokokin jihohi 36 na }asar nan sun za~e shi har sau biyu a matsayin Shugaban {ungiyar Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohi ta {asa, wannan ya }ara tabbatar da gogewarsa a fagen shugabanci. Yana cikin muhimman mutanen da suka bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban jihar Filato. A lokacin da yake ri}e da mu}amin shugaban Majalisar Dokokin jihar ne ya jagoranci samar da jami’a mallakar jiha wadda aka sauyawa suna zuwa Jami’ar Solomon Lar, da sauran ayyukan ci gaban al’umma da suka sanya shi ya kasance abin alfahari ga mutanen jihar. Kamun ludayin mulkinsa a matasayin Gwamnan jihar daga watan Mayun shekarar 2015 zuwa yau ta sanya tun da da]ewa al’ummar jihar suka soma ganin farar safiya a jihar ta Filato. Yanzu haka yana cikin ]ai]aikun gwamnonin da suka fi }arfin nunawa da ]an yatsa muddin ana maganar aiki da cikawa ta fuskar ci gaba.

7. Farfesa Abdallah Uba Adamu (Shugaban Jami’ar NOUN) Farfesa Abdalla Uba Adamu shi ne shugaban Jami’ar nan da ke tafiyar da tsarin karatu daga gida wato NOUN. Yana cikin manyan masana kuma shaihunan malamai da suka shahara a fagen bincike-bincike, neman ilimi da kuma ya]a shi a cikin al’umma. Ya da]e yana bayar da gudummawa a fannoni daban-daban na ilimi ciki kuwa har da fagen fasahar sadarwar ta zamani da fannin adabi da sauransu wa]anda za a iya cewa duk da kasancewa ba fagensa ba ne, ya bayar da gudummawar da ta zarta ta wasu masana da suka goge a fagagen. Ya kafa tarihin kasancewa ]aya daga cikin ‘yan }alilan na shaihunan malaman da }wazonsu da gogewarsu tare da tarin gudummawarsu ga duniyar ilimi ta sanya su samun matsayin farfesa har guda biyu. Da farko dai Abdalla Uba Adamu farfesa ne a fannin ilimin malantar kimiyya tun a shekarar 1997 wanda nan ne fagen da aka fi saninsa a kai, kasancewarsa gonarsa ta noman ilimi, haka ma farfesa ne a fagen sadarwa da kuma al’adu wanda Jami’ar Bayero ta ba shi a shekarar 2012. Farfesa Abdalla Adamu ]an asalin jihar Kano ne da aka haifa a ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 1956, yana da digirin farko a ilimin malantar kimiyyar halittu da ya samu a shekarar 1979 daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, digirinsa na biyu ma a fannin malantar ilimin kimiyya ne daga Jami’ar Landan a shekarar 1982, yayin da ya samu digirin digirgir daga Jami’ar Sussex University, Falmer, Brighton, da ke Ingila. Tun daga shekarar 1981 Farfesa Abdalla yake aikin koyarwa a matakai daban-daban a Jami’ar Bayero ta Kano da sauran jami’o’in ciki da wajen }asar nan. Haka ma ya taka rawa muhimmiya a sassan mulki da shugabanci da kuma nazarce-nazarce da bincike- binciken ilimi daban-daban. Shi ne ya }ir}iri manhajar nan ta ABDALLAH da ake amfani da ita akan na’urar kwamfuta wajen rubutun Hausa wadda ke ]auke da haruffan ‘{‘ da ‘[‘ da’|’ da ‘]’ da ‘}’ da ‘~’. Yanzu haka da yake shugabancin wannan Jami’ar ta NOUN, Shaihin malamin ya samu nasarar baje kolin haza}arsa da gogewarsa wajen ]ora wannan jami’a akan turbar ci gaba. Daga lokacin da ya kar~i shugabancin Jami’ar zuwa yau an samu gagarumin ci gaba wajen }ara samun kar~uwar tsarin karatunta wanda a baya wasu al’umma suka jahilta wasu kuma suke yin ]ari-]ari wajen rungumarsa. Yawan kwararowar ]aliban da jami’ar ke samu da kuma }ara ingancin ilimin da take samarwa da ma gudummawar da take bayarwa ga ci gaban ilimi a }asar nan ya sanya sunan Farfesa Abdalla Uba Adamu ya }ara haskawa a matsayin wani jigon raya ilimi da watsa shi ga al’umma.

8. Farfesa Mahmud Yakub (Shugaban Hukumar Za~e ta {asa INEC) A ranar 21 ga watan Oktoban shekarar 2015 ne Shugaban {asa Muhammadu Buhari ya tabbatar da na]in Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban Hukumar Za~e mai zaman kanta ta {asa wato, INEC. Farfesa Yakubu, wanda ]an asalin jihar Bauchi ne, gogaggen masanin ilimin tarihi ne, kuma ]aya daga cikin manyan shaihunan malaman tarihi da Nijeriya da ma nahiyar Afurka ke matu}ar bugun gaba da su. Shaihin Malami ne a fannin tarihin siyasa da harkokin }asa da }asa, haka kuma masani ne akan harkokin ya}i da ta’addanci. Ya sha lashe lambobin yabo iri-iri a matsayin manazarci mafi nuna }wazo da jajircewa a fagen bincike-binciken ilimi wa]anda Kwamitin Mataimakan Shugabannin Jami’o’in {asar Ingila suke sanyawa domin fitar da zakaru a cikin manyan manazarta ilimi a tsakanin ]alibai masu karatu a }asashen }etare. Gabanin na]insa a matsayin Shugaban Hukumar Za~e ta INEC, Farfesa Yakubu ya ta~a zama Babban Sakataren Asusun raya ilimin manyan makarantu na TETFund a shekarar 2007, inda a nan ma ya bayar da gagaruwar gudummawa ga ci gaban ilimin gaba da sakandare a }asar nan. Kamun ludayin shugabancinsa a Hukumar Za~e ta INEC ya da]a fitowa da }warewarsa da kuma gogewarsa a fagen shugabanci, za~u~~ukan da hukumar ta gudanar na cike gurbi a wa]ansu jihohi da kuma za~u~~ukan da aka gudanar na gwamnonin jihohin Bayelsa da Edo da kuma Ondo sun kasance wata manuniya akan irin yadda shaihin malamin ya tsaftace tare da daidaita sahun harkokin za~e a }asar nan tare da tabbacin cewa samun sahihin za~e a Nijeriya al’amari ne mai sau}i muddin tafiyar ta ]ore a yadda take a }ar}ashin shugabancin Hukumar a yau.

9. Daktar Maikanti Kachalla Baru (Shugaban Kamfanin Mai na NNPC) Injiniya Dakta Maikanti Baru wanda yanzu haka shi ne shugaban Kamfanin mai na }asa wato, NNPC, gogaggen ma’aikacin Kamfanin ne wanda ya kwashe tsawon lokaci yana bayar da gagarumar gudummawa a ayyukan kamfanin a sassa daban-daban da ya yi aiki a ciki. Ya ta~a ri}e matsayin Babban Manajan Matatar mai ta Greenfield Refinery, haka ma ya ri}a mu}amin Manajan Darakta a kamfanin Hyson, haka ma ya ta~a zama Babban Daraktan Kamfanin Iskar Gas na {asa wato NGS. Kafin na]insa a matsayin Shugaban Kamfanin na NNPC, Dakta Maikanti Baru yana ri}e ne da mu}amin Babban Darakta a fannin ha}owa da kuma sarrafa mai na Kamfanin. Injiya Dakta Maikanti Baru yana da digirinsa na farko a fannin injiniyanci wanda ya samu daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, haka ma yana da digirin digirgir duk dai a fannin inijiniyanci, wa]anda suka kasance masa sinadarin samun nasara a dukan fannoni ko kuma sassan da ya yi aiki a ciki. Daga lokacin da Dakta Maikanti Baru ya kar~i ragamar tafiyar da kamfanin mai na NNPC, an samu gagarumar nasara a fannin samarwa da kuma sarrafa mai a }asar nan. Yawan ku]a]en shiga da ake samu da kuma tabbatar da cewa ku]a]en suna shiga aljihun gwamnati shi ma ya inganta, haka kuma wadata al’umma da mai tare da magance }arancinsa ta hanyar tabbatar da samun wadataccen mai ga al’umma ba tare da yankewa ba shi ma wani namijin }o}ari ne irin na yabawa daga shugabancin nasa. {o}arin magance matsalar yawaitar yajin aikin masu ruwa da tsaki a harkokin mai a }asar nan wanda ya sha kassara jin da]in jama’a da shi kansa tattalin arzikin }asa, wata ho~~asa ce da ta da]a tabbatar da kaifin basirar Dakta Maikanti wajen fahimtar cewa sanin wurin bugu shi ne }ira.

10. Farfesa Danbala Danju (Shugaban Bankin Manoma na BOA) Farfesa Danju [anbala shi ne Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Bankin Ha~aka Harkokin Noma na BOA, gogaggen masanin }abli da ba’adin sha’anin tattalin arziki ne wanda ke da mallakin mabambantan digiri har ma da digirin digirgir a fannin tsimi da tanadi. Haifaffen garin Tofa ne da ke cikin jihar Kano ta Arewacin Nijeriya, wanda aka haifa a ranar 23 ga watan Maris na shekarar 1962. Shaihin malamin yana da digirinsa na farko a fannin tattalin arziki da ya samu daga Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 1985. Digirinsa na biyu ma a fannin na tsimi da tanadi ne duk dai daga Jami’ar ta Bayero a shekarar 1989. Ya samu digirinsa na digirgir daga Jami’ar nan ta Bradford da ke {asar Ingila a shekarar 1997. Farfesa Danju }warrarren mashawarci ne da ya zama tamkar wata madogara a duk lokacin da aka zo zancen harkokin tattalin arziki ko kuma tu’ammalin ku]a]e, yanzu haka babban shawarci ne a ofishin Babban Daraktan da ke wakiltar }asashen Nijeriya da Sao Tome & Principe a bankin nan na raya }asashen nahiyar Afurka wato African Development Bank. Farfesa Danju [anbala mutum ne da gudummawarsa da kuma hidimarsa ga jama’a ba ta ta}aita ga wani yankin al’amurran yau da kullum ba kurum, domin kuwa kafin shigarsa cikin Hukumar Daraktocin Bankin na ADB a shekarar 2009, Farfesan ya yi aiki da kamfanin ha}o mai na Exxon Mobil, haka ma ya ta~a zama Shaihin Malami a Sashen Tsimi da Tanadi na Cibiyar Harkokin Bincike da Nazarin Tsimi da Tanadi ta Kazakhstan Institute of Management, Economics and Strategic Research, (KIMEP) da ke {asar Kazakhstan da ke yankin Tsakiyar nahiyar Asiya. Bankin Bun}asa Harkokin Noma na BOA da Farfesa [anbala ke shugabanci na sahun gaba wajen tallafawa yun}urin bun}asa aikin gona da yanzu haka gwamnati ta himmatu a kai, a matsayinsa na ]an Arewa, mai kishin Arewa, mai son ganin bun}asuwar tattalin arzikin Arewa, Farfesa [anbala na amfani da matsayinsa na shugabancin wannan Banki wajen taimakawa tattalin arzikin wannan yanki da kuma jama’arsa da akasarinsu suka dogara ga harkokin noma da kiwo.

11. Ibrahim Mustapha Magu (Shugaban Hukumar EFCC) Sunan Ibrahim Mustapha Magu ba ~oyayye ba ne, ba kuma ba}o ba ne ga duk wani ]an }asar nan, ba yadda za ka iya raba nasarar ya}i da cin hanci da gwamnatin Shugaba Buhari ke samu da namijin }o}arin Ibrahim Magu, wanda shi ne ke shugabantar Hukumar. Hazi}in jami’in Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ne da aka yi wa shaidar rashin tsoro ko fargaba wajen gudanar da aikinsa. {warewar da yake da ita ta gogaggen akanta kasancewar ya mallaki digiri a fannin akantanci da ya samu daga Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1986 ta bayyana fili a irin yadda Hukumar ta EFCC ke tafiyar da ayyukanta cikin nasara da }warewa. Har ila yau Ibrahim Magu wanda ]an asalin }abilar Kanuri ne daga jihar Borno, }wararren masanin harkokin tu’ammalin ku]a]e ne kuma hazi}in mai binciken }wa}waf akan laifukan da suka ji~inci almundahanar ku]a]e wanda ya samu horo mai zurfi daga cibiyar hukumar nan ta FBI mai binciken manyan laifuka ta Amurka da kuma Cibiyar horas da jami’an ‘yan sanda ta Birnin Landan. Haka ma ya samu babbar takardar shaida akan ya}i da ayyukan cin hanci daga Jami’ar Hong Kong, sai kuma digiri na biyu akan tabbatar da bin doka da binciken manyan laifuka da ya samu daga Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 2011. Ibrahim Magu mutum ne mai kaifin basira da }wazon aiki wanda tun gabanin ya zama shugaban Hukumar ta EFCC yake taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar binciken-binciken Hukumar. Nasarar da yanzu haka ake samu wajen }wato dukiyar da wasu gur~atattun jama’a suka yi rub da ciki a kai da kuma samun raguwar satar dukiyar jama’a da yanzu haka ake samu duk yun}uri ne da ya kamata a jinjinawa Ibrahim Magu a kai. Babu shakka idan za a bayar da lambar gwarzon madugun ya}i da ayyukan cin hanci da sauran laifukan da suka shafi almundahanar ku]a]e a }asar nan a sheakarar 2016, to, babu shakka Ibrahim Magu ne mafi dacewa da kuma cancantar kar~ar wannan kambun.

12. Sheikh Dakta Isah Ali Pantami (Shugaban Hukumar NITDA) Da yawan jama’a sun fi sanin sunan Sheikh Dakta Isah Ali Pantami a matsayin mashahurin malamin addini da ya yi fice wajen wa’azin addinin Musulunci da kuma ya]a iliminsa a tsakanin al’umma. To, sai dai wani abu da watakila wasu ba su sani ba game da malamin shi ne, ko baya ga zurfin iliminsa na addinin Musulunci, shaihin malamin ilimin na’ura mai }wa}walwa ne a Jami’ar Musulunci ta Madina da ke {asar Saudi Arebiya. Hasali ma shi ne ]an Nijeriya na farko a tsawon tarihin kafuwar Jami’ar na tsawon shekaru 63 da ya samu damar koyarwa a wannan Jami’a. Farfesa Isah Pantami wanda ba da da]ewa ba Shugaban {asa Muhammadu Buhari ya na]a shi a matsayin Shugaban Hukumar Bun}asa Fasahar Sadarwar Zamani ta NITDA, ]an asalin jihar Gombe ne, kuma yana da mallakin digirin farko a fannin na’ura mai }wa}walwa da ya samu daga Jami’ar Abubakar Tafawa |alewa ta Bauchi a shekarar 2002, sai kuma digiri na biyu duk dai daga wannan Jami’ar kuma a fannin na’ura mai }wa}walwa da ya samu a shekarar 2008. Ya }ara samun wani digiri na biyu a fannin fasahar kasuwanci daga wannan jami’ar a shekarar 2010. Digirinsa na Dakta kuwa ya same shi a {asar Ingila. Sheikh Isah Pantami masani ne da ya bayar da gagarumar gudummawa a dukkan sassan ilimi biyu da ya }ware a kai, wato ilimin addini da na zamani. Ya yi rubuce-rubuce da dama a cikin kowane ~angare, haka ma ya gabatar da }asidu da ma}aloli da nazarce-nazarce da bincike-bincike a cikin harsunan Turanci, Larabci da kuma Hausa wa]anda ]aliban ilimin addini da na zamani, musamman a fannin kimiyya ke ci gaba da fa’idantuwa da su. Yana daga cikin jerin 'Yan Arewa da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban yankinsu da }asa baki ]aya a shekarar da ta gabata.

13. Farfesa Aminu Ibrahim (Shugaban Kwalejin Fasaha da {ere-{ere ta Umaru Shinkafi) Farfesa Aminu Alhaji Ibrahim, Shugaban Kwalejin Fasaha da {ere-{ere ta Umaru Ali Shinkafi da ke Sakkwato wata ajiyar Allah ce kuma wani kogi a fagen ilimi wanda ya samu shahara da ]aukaka a ciki da wajen }asar nan a fannin ilimin lissafi. Shaihin malamin ya kwashe shekaru yana bayar da muhimmiyar gudummawa ga duniyar ilimin kimiyya ta hanyar bincike da nazari da koyarwa da kuma rubuce-rubuce da suka kasance madogara ga ]aliban ilimi da manazarta. Farfesa Aminu ya fito daga unguwar Kanwurin Daku dake cikin }waryar birnin Sakkwato, an haife shi ne a shekarar 1966, ya yi karatunsa na furamare a makarantar Nizzamiyya dake unguwar Sabon Birni daga shekarar 1972 zuwa 1979, ya halarci makarantar sakandaren ilimin kimiyya ta musamman wadda a yau aka sauyawa suna zuwa sakandaren Sani Dingya]i dake Farfaru daga shekarar 1980 zuwa 1984. Ya samu digirinsa na farko a fannin lissafi daga Jami’ar Usmanu [anfodiyo a shekarar 1988, shi ma digirinsa na biyu a fannin lissafin ne wanda ya samu daga Jami’ar Legas a shekarar 1993, daga nan sai ya sake dawowa Jami’ar Usmanu [anfodiyo inda ya samu digirin digirgir wato Dakta a fannin lissafi a shekarar 2005. Ko bayan wa]annan Farfesan yana da takardar shaidar Babbar Difiloma a fannin akantanci daga Jami’ar Ahmadu Bello da kuma digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Usmanu [anfodiyo. Ya soma aikin koyarwa tun a shekarar 1990 inda ya yi aiki a a matsayin malamin lissafi a tsohuwar Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Jiha, wadda ta riki]a zuwa Kwalejin Fasaha ta Umaru Shinkafi a yau. Daga bisani ya koma sashen lissafi na Jami’ar Usmanu [anfodiyo a matsayin malami inda ya ci gaba da taka matakan ilimi har ya kai }olulowar }urewa bayan da ya samu zama farfesan ilimin lissafi a shekarar 2010. Ko bayan aikin koyarwa, Farfesa Aminu ya ri}a mu}amai da dama a sassa daban-daban na Jami’ar ta Usmanu [anfodiyo. A lokacin da aka kafa sabuwar Jami’ar Jihar Sakkwato, Farfesa Aminu ya kasance ]aya daga cikin ginshi}an masanan da aka gayyato domin bayar da gudummawarsu ga tsayuwar Jami’ar inda ya kasance shugaban tsangayar kimiyya ta Jami’ar, daga bisani kuma aka za~e shi a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar na fannin tsare- tsaren ilimi, matsayin da yake ri}e da shi har zuwa farkon shekarar 2016 lokacin da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta na]a shi a matsayin Shugaban Kwalejin Fasaha ta Umaru Ali Shinkafi. Farfesa Aminu ya sha samun lambobin yabo da kuma kambun karramawa a matsayin wani gwarzon masani a duniyar lissafi, kambun baya-bayan nan da ya lashe shi ne na gwarzon kuma hazi}in da ya fi yin fice wajen bayar da gudummawa ga ci gaban ilimin kimiyya da }ere-}ere wanda {ungiyar ISESCO ta shirya a shekarar 2016 inda ya fafata tare da doke mashahuran shaihunan malaman kimiyya daga jami’o’i daban-daban na sassan duniya.

14. Alhaji Ibrahim Commassie (Sardaunan Katsina) Alhaji Ibrahim Commassie, na sahun gaba a cikin fitattun ‘ya’yan yankin Arewa da suka taka muhimmiyar rawa ga ci gaban }asar nan, wa]anda tuni sunansu ya samu gurbin zama na din-din-din a kundin tarihin Nijeriya. Commassie ya yi fice a matsayin ]aya daga cikin Manyan Sufetocin ‘Yan Sandan Nijeriya da suka bayar da }arfinsu da lokacinsu wajen ]ora sha’anin aikin [ansanda akan madaidaicin tafarki. Yanzu kuma yana ]aya daga cikin manyan dattawan da yankin na Arewa ke alfahari da su. Tun daga watan Mayun shekarar 1999 da Alhaji Ibrahim Commassie ya yi sallama da aiki, bayan kwashe tsawon shekaru yana yi wa }asarsa da jama’arsa hidima. Ya du}ufa ainun wajen ganin ya ci gaba da tsayuwa akan a}idarsa ta amfani da duk wata dama ko kafa da mutum ya samu, domin taimakawa ga inganta rayuwar jama’arsa daidai gwargwadon hali. Tun daga wancan lokaci zuwa yau, Alhaji Ibrahim Commassie ya ci gaba da tabbatar da kishinsa ga jama’a inda ko a shekarar 2004, Masarautar Mai Martaba Sarkin Katsina, ta na]a shi shugabancin kwamitin bun}asa aikace-aikacen {ungiyar Jama’atul Nasrul Islam a jiharsa ta haihuwa, wato Katsina. Haka ma memba ne na kwamitin amintattu na Dandalin Tuntu~a na Arewa, wato ACF, a jihar Katsina, inda a nan ma yake bayar da muhimmiyar gudummawa ga }are muradu da bu}atun yankin Arewa da jama’ar Arewa. Alhaji Ibrahim Commassie, mutum ne da ya yi amanna da cewa samun ingantaccen ilimi, shi ne }ashin bayan samuwar ci gaban duk wata }asa ko al’umma, don haka ya yi tsayin daka wajen ]aukar wannan fannin domin samar masa gata da irin ]an abin da Allah ya huwace masa. Ya sha tallafawa ci gaban ilimi a matakai daban-daban. A irin wannan }o}arin ne, Alhaji Ibrahim Commassie ya samar da kayan bincike na miliyoyin nairori ga ]akunan binciken kimiyya na Makarantar Sakandaren ‘Ya’yan ‘Yan Sanda ta maza da ke garin Mani ta jihar Katsina. Wannan }ari ne akan ]imbin gudummawarsa ga ci gaban ilimin ‘ya’yan marasa }arfi a matakai da fannoni daban- daban, wanda sanin adadin wa]anda suka shiga cikin wannan yalwatacciyar inuwa ta Alhaji Ibrahim Commassie, ba abu ne mai sau}in bayyanawa ba. Yabawa da }wazo da kuma gudummawarsa ga jama’a, ya sa a can baya, masarautar Mai Martaba Sarkin Katsina ta na]a Alhaji Ibrahim Commassie a matsayin Sardaunan Katsina, ]aya daga cikin manya-manya kuma jiga-jigan ginshi}an masarautar Katsina.

15. Alhaji Mamman Daura Matsayin uba yake ga Shugaba Muhammadu Buhari duk da kasancewar tazarar shekarun da ke tsakaninsu ba ta kai shekara uku ba, Mamman Daura }ani ne ga mahaifin Shugaba Muhammadu Buhari. Sha}uwarsu da kusancinsu ga juna abubuwa ne da suka da]e suna ]aukar hankalin masu lura da dangantakar mutanen biyu tun daga }uruciya zuwa samartaka zuwa manyanci har zuwa dattijantaka. Da yawa ana duban Alhaji Mamman Daura a matsayin wani }usa kuma mai matu}ar }arfin fa]a a ji a duk wani abu da Shugaba Buhari zai yi, ko zai }i yi, ko dai a farfajiyar mulki ko kuma ta hul]ar yau da kullum. A ta}aice za a iya cewa Mamman Daura na cikin mutane ‘yan }alilan da Shugaba Buhari ya aminta da su, wa]anda kuma yake matu}ar ganin kimarsu da mutunta su, wannan ne ya sa wasu ke ganin Mamman Daura a matsayin wani mutum ]aya tilo da sitiyarin tafiyar da gwamnatin Buhari ke hannunsa ta yadda duk wata kwana ko wani hawa da ganganra da za a yi, suna dogara ne da irin al}iblar da ya juya akalar tafiyar. Wannan ne ya sa sunansa ya yi tambari har ta kai da yawan jama’a suka san sunansa gabanin sanin fuskarsa. Alhaji Mamman Daura dai hamsha}in ]an kasuwa ne ta ~angaren masana’antu, mutum ne da aka yi wa shaidar kaifin basira da haza}a a dukan al’amuransa. Ya ta~a zama cikin mashawartan Shugaba Buhari a zamanin mulkinsa na soji a shekarar 1983. A }arshen shekarun 1980 kuwa, Mamman Daura ya kasance shugaban bankin African International Bank wanda a lokacin marigayi tsohon Sarkin Musulmi, Alhaji Ibrahim Dasuki ke shugabanta, haka ma ya ta~a zama shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Gidan Talabiji ta NTA, kafin sannan ma ya ta~a zama editan jaridar New . Alhaji Mamman Daura ya taka muhimmiyar wajen samun nasarorin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, musamman a shekarar da ta gabata.

16. Farfesa Ango Abdullahi Dattijo Farfesa Ango Abdullahi, mai kimanin shekaru 79 a duniya, haifaffen }auyen Yakadawa ne da ke cikin masarautar Zazzau mai da]a]]en tarihi. [aya daga cikin manyan dattawan Arewa da suka yi fice wajen kare muradin yankin, komai wuya komai rintsi. Masani ne kuma shugaban da ya sadaukar da tunaninsa da lokacinsa da basirarsa da }arfinsa a jiya da yau wajen ciyar da yankin Arewa da kuma al’ummar yankin a gaba. An haife shi ne a cikin shekarar 1938 miladiyya. Farfesa Ango na cikin fitattun ]aliban shaharriyar Kwalejin Barewa dake Zariya, kwalejin da ta yaye fitattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa a sassa daban-daban na rayuwar al’umma wanda shi kansa shaihin malamin, yana ]aya daga cikinsu. A shekarar 1958 ne dai Farfesa Ango Abdullahi ya kammala karatunsa a Kwalejin ta Barewa, daga nan sai ya shiga Kwalejin Nijeriya dake Zariya, wato Nigerian College Zaria, domin zurfafa iliminsa. Ya halarci Jami’ar Ibadan, wadda a lokacin ita ce jami’a ]aya tilo a }asar nan, kasancewar ta wani sashe na Jami’ar Landan. Haka ma, ya halarci Jami’ar Kansas dake }asar Amurka. Ya zama cikakken shaihin malami, wato Farfesa a fannin aikin gona, sa’annan kuma Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, tun daga shekarar 1979 har zuwa 1986. Bayan kammala wa’adin shugabancin jami’a, Farfesa Ango Abdullahi, ya yi amfani da tarin iliminsa da kuma }warewarsa a fannin sha’anin noma, domin fitowa da ingantattun hanyoyin da za su ciyar da sha’anin noma gaba, al’amarin da zai taimaka wajen farfa]owa da harkar noma da samar da ayyukan yi ga matasa da kuma uwa uba, }ara }arfin tattalin arzikin }asa. Har gobe, yana gaba-gaba a sahun wa]anda ke sukar raggon azancin salo da tafarkin tafiyar da tattalin arzikin }asa mai fasalin kaifi ]aya da ke neman mamaye sha’anin tattalin arzikin }asar nan. Farfesa Ango Abdullahi, ya sha samun yabo da jinjina daga }ungiyoyin jama’a da hukumomi da shugabanni da kuma ita kanta gwamnati. Yana da lambar karramawa ta CON, wanda Gwamnatin Tarayyar }asar nan ta ba shi a shekarar 2007, haka ita ma Masarautar Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, ta na]a Farfesa Ango Abdullahi a matsayin Magajin Rafin Zazzau duk a cikin shekarar ta 2007.

17. Sanata Ahmad Lawal Sanata Ahmad Ibrahim Lawal ba }ashin yadawa ba ne a fagen siyasa, shugabanci da wakilcin jama’a. Sanatan wanda yanzu haka shi ne Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa ta }asa, yana wakiltar Maza~ar Yobe ta Arewa ne a Majalisar tun daga shekarar 2007 har zuwa yau. Kafin zuwansa Majalisar Dattawa, Sanatan ya kwashe shekaru takwas cur yana wakilcin maza~arsa a zauren Majalisar Wakilai ta }asa tun daga shekarar 1999 da }asar nan ta dawo kan mulkin dimokura]iya har zuwa shekarar 2007 inda a tsakanin wannan zango ya ri}a mu}amin shugaban kwamitocin ilimi da na aikin gona a Majalisar ta Wakilai. An haifi Sanata Ahmad Lawal a cikin shekarar 1959, ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Gashua ta jihar Yobe, da Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Yana da mallakin digiri na ]aya har zuwa digirin digirgir a fannin nazarin }asa wato Geography, ya yi aikin koyarwa a Jami’ar Maiduguri na tsawon shekara 10 wato daga shekarar 1987 zuwa 1997, kafin ya ajiye aiki ya tsunduma harkokin siyasa. Sanata Ahmad Lawal na cikin manyan jigan-jigan siyasar adawa kasancewa tun shigowarsa fagen siyasa a shekarar 1999 ya ke ~angaren adawa har zuwa lokacin da tsohuwar jam’iyyarsa ta ANPP ta ha]e da wasu jam’iyyun siyasa domin samar da jam’iyyar mai mulki a halin yanzu wato APC. Kasancewar Sanata Lawal cikin jerin manyan tsofaffin hannu a Majalisa ya sanya shi kasancewa ]aya daga cikin ginshi}an Majalisar wa]anda ke da kima a idon membobin Majalisar. Yana kan a jerin ‘yan Majalisar da aka sa ran su ]are kujerar Shugabancin Majalisar bayan }addamar da ita a watan Yunin shekarar 2015, haka kuma duk da kasancewa hakan ba ta samu ba, Sanata Lawal ya ci gaba da kasancewa cikin jerin ‘yan Majalisar Dattawa na jam’iyyar APC masu }arfin fa]a a ji a zauren Majalisar.

18. Sanata Shehu Sani Kafin tsundumarsa harkokin siyasa gadan-gadan, Sanata Shehu Sani ya fi yin fice ne a matsayin ]an gwagwarmayar tabbatar da dimokura]iyya kuma sanannen mai fafatukar kare ‘yancin al’umma dake zaune a jihar wanda sanadiyar nacinsa da fito-na-fitonsa ga hukumomi wajen ganin an yi komai akan gaskiya, ta sa gwamnatocin soji da dama da suka gabata suka sha gar}ame shi a jarun, har ta kai ma ko da }asar nan ta sake dawo wa akan mulkin dimokura]iyya a shekarar 1999, Kwamared Shehu Sani yana zaman wa}afi ne na ]aurin rai da rai kafin gwamnatin da ta zo kan mulki ta sallame shi. Sanata Shehu Sani yana wakiltar al’ummar maza~ar Kaduna ta Tsakiya a }ar}ashin jam’iyyar APC, yana cikin membobin Majalisar Dattawa da suka fi ]aukar hankalin jama’a, musamman yadda yake fitowa }arara yana sukar lamiran gwamnati mai mulki duk kuwa da kasancewarsa ]an jam’iyya mai mulki, al’amarin da salon tafiyar siyasar Nijeriya bai gada ba. A}idarsa da salon tafiyar siyasarsa sun samar masa mabambantan matsayi a wurin al’umma, a yayin da wasu ke yi masa duban jarumi kuma gwarzon ]an siyasar a}ida, wasu na yi masa fassarar wani ]an siyasar taratsi mai bahaguwar al}ibla. Yanzu haka dai Sanata Shehu Sani na cikin jerin ‘yan Majalisar Dattawa da suka fi yin fice ba wai daga yankin Arewa ba kurum, har ma da }asa baki ]aya.

19. Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure Honarabul Muhammadu Gudaji Kazaure na sahun gaba a cikin ‘yan Majalisar Tarayya da suka fi ]aukar hankalin jama’a cikin shekarar 2016 duk kuwa da kasancewarsa ]aya daga sababbin hannu a zauren Majalisa. An haifi Honarabul Gudaji Kazaure a shekarar 1972, ya samu takardar shaidar kammala karatun sakandare a shekarar 1994 daga Sakandaren Gwamnati ta Dala da ke Kano. Kafin shigowarsa harkokin siyasa, Honarabul Kazaure ya yi aikace-aikace da harkokin kasuwanci na tsawon shekaru. Gogagge ne a fagen hada-hadar shigowa da kuma tantancewa da kaya, har ma ya ta~a amsar lambar yabon Hukumar Kwastan ta {asa a wannan fanni a shekarar 2004, a matsayin mafi ingancin ejen na tantance kaya a Tashar Ruwa ta Tincan da ke Legas. Haka ma ya yi aikin samar da rijiyoyin burtsatse a sassa daban-daban na }asar nan. Honarabul Gudaji Kazaure har ila yau tsohon jami’in rundunar ‘yan sandan Nijeriya ne wanda ke da }warewa wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a. A shekarar 2015 ne aka za~e shi a matsayin [an Majalisar Tarayya mai wakiltar maza~ar }ananan hukumomin Kazaure da Roni da Gwiwa da ‘Yankwashi da ke Jihar Jigawa.

20. Honarabul Abdulmuminu Jibril Honarabul Abdulmuminu Jibril ya yi fice ainun bayan }urar da ya tayar dangane da kasafin ku]in shekarar 2016 da ta gabata. [an Majalisar Wakilan wanda yanzu haka yake zaman wa’adin hutun dole da Majalisar ta tura shi sakamakon wannan }urar da ya tayar, yana wakiltar Maza~ar Tarayya ta }ananan hukumomin {iru da Bebeji dake jihar Kano, har ila yau kuma shi ne tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Ku]i na Majalisar a wancan lokaci. Mai kimanin shekaru 41 a duniya, Honarabul Jibril matashin ]an siyasa ne, malamin makaranta kuma gogaggen ]an kasuwa. An soma za~ensa zuwa Majalisar Tarayya a shekarar 2011 a inuwar jam’iyyar PDP, an sake za~arsa a karo na biyu akan wannan matsayi a shekarar 2015 a inuwar jam’iyyar APC, inda a lokacin ne aka ba shi shugabancin Kwamitin Kasafin Ku]i na Majalisar kafin ya bayar da sanarwar ajiye mu}amin biyowa bayan hayagagar da ta taso ta zargin aringizon al}aluman kasafin ku]in shekarar 2016. Daga bisani a ranar 28 ga watan Satumbar shekarar ta 2016, Majalisar ta bayar da sanarwar dakatar da shi daga halartar zaman Majalisar har na tsawon kwanakin zaman Majalisa 180, saboda abin da majalisar ta kira rashin ]a’a da biyayya ga dokokin Majalisa. Honarabul Jibril wanda ke ri}e da sarautar Jarman Bebeji, mutum ne da ko baya ga harkokin siyasa da kasuwanci da kuma aikin koyarwa, yake kan ayyukan tallafawa marasa galihu. Yana cikin matasan ‘yan siyasar da suka yi fice a shekarar 2016.

21. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar {oli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, uba ne kuma shugaba da tasirinsa ya tsallake yankin Arewa ko ma Tarayyar Nijeriya, tamkar yadda tasiri da }arfin fa]a a ji na Masarautar da yake mulki ya tsallaka har zuwa sassan duniya da dama. Gudummawarsa a matsayin shugaban al’umma kuma jagoran al’ummar musulmin Nijeriya ba za ta yi sau}in kwatantawa ba, musamman rawar ya ke takawa wajen samun daidaituwar al’amurra a ciki da wajen }asar nan. Mai alfarma Sarkin Musulmi ya taka muhimmiyar rawa a fagen ayyukan raya addinin Musulunci tare da samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin da mabiya sauran addinai da ke ciki da wajen }asar nan. Gudummawarsa wajen tabbatar da ha]in kai da fahimtar juna a tsakanin al’ummar Musulmin Nijeriya mabiya mazhabobi da ]ariku daban-daban da kuma tabbatar da kyakkyawar hul]a da fahimtar juna tsakanin al’ummar Musulmin }asar nan da mabiya sauran wasu addinai babban abin yabawa ne. {o}arinsa wajen tabbatar da nasarar ya}i da cutar shan inna wadda sanadiyar sa ne Nijeriya ta samu nasarar ficewa daga jerin }asashen da Hukumar Lafiya ta Duniya wato, WHO ta bayyana a matsayin matattarar cutar ta shan inna zai kasance al’amarin da tarihi ba zai ta~a mantawa da shi ba. Ko baya ga wannan Mai Alfarma Sarkin Musulmi na taka rawa a sassa daban-daban da suka ha]a da na zaman lafiya da siyasa da tattalin arziki da kuma uwa uba sha’anin addini. Namijin }o}arinsa wajen daidaita tsakanin al’umma da magance matsalar rikice-rikicen siyasa da na }abilanci da tashin-tashiyar manoma da makiyaya, ya }ara ]aga darajarsa da matsayinsa da kimarsa da dattakunsa a idon al’umma.

22. Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, na daga cikin manyan sarakunan masarautun Arewa da suka yi fice, suka kuma taka muhimmiyar rawar a zo, a gani, a kuma yaba a sassa daban-daban na rayuwar al’ummar da suke mulki da ma su kansu Masarautun na su. Mai Martaba Sarki yana sahun gaba wajen ankarar da ~angaren shugabanci akan duk wani abu da yake ganin ya dace a yi, ko kuma matakan da ya kamata a ]auka domin inganta rayuwa da jin da]in jama’a, wannan na daga cikin abubuwan da suka }ara masa fice tare da tagomashi a idon jama’a. Ko baya ga ci gaban da ya samar a matsayin da yake a kai na Sarautar Masarautar Kano, tarihin jagorancinsa ga duk wani al’amari da aka shugabantar da shi a kai cike yake da nasarori. Alal misali, matsayin da ya ri}e na Amirul Hajjin shekarar 2015, ya }ara fitowa da shi a matsayin jagora abin kwaikwayo, duk da irin tangar]ar da aka fuskanta a a lokacin gudanar da ayyukan Hajjin na shekarar, an samu kyakkyawar gamsuwa da irin shugabancinsa ga tawagar alhazan }asar nan da kuma gagarumar gudummawarsa wajen samun nasarar aikin na hajji. Haka ma shugabancin da ya yi ga bikin cikar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III shekara 10 akan mulki shi ne ya da]a tabbatar da ingancin salon tafiyar da mulkinsa. Uwa uba, salon tafiyar da mulkinsa a Masarautar Kano ya }ara fitowa da martabar Masarautar mai ]imbin tarihi da kuma tasiri a tsakanin masarautun }asar nan. Ko ka]an San Kanon bai ta~a }asa a gwiwa ba wajen tsage gaskiya komai ]acinta musamman ga shugabanni da mafi yawan jama'a ke shakkun fuskantarsu domin gaya masu gaskiya.

23. Mai Martaba Sarkin Borgu Muhammadu Sani Haliru Dantoro Kitoro IV Mai Martaba Sarkin Borgu Alhaji Muhammadu Sani Haliru [antoro Kitoro na IV shi ne Sarkin Masarautar Borgu na 17 kuma ]a ga tsohon Sarkin Borgu Alhaji Muhammadu Haliru [antoro Kitoro na III wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2015 a wata asibiti dake }asar Jamus. Kafin na]insa akan wannan matsayi, Sarkin na Borgu wanda }wararren lauya ne, yana ri}e da saurautar Marafan Borgu, kuma ya fito ne daga gidan sarautar Masarautar na Gbemusu. Sabon Sarkin wanda ke da shekaru 51 a duniya, sarki ne da za a iya cewa ba wai sarautar shahararriyar Masarautar Borgu kawai ya gada ba daga mahaifinsa, har ma kwarjini da matsayi irin wanda mahaifinsa ya rayu akai, ba wai a tsakanin masu ri}e da manyan masarautun jihar Neja ba kurum har da a matakin }asar ga baki ]aya. Kasancewar akwai tarihin }ulluwar aminci da soyayya tsakanin Masarautar ta Borgu da kuma marigayi mahaifinsa da Shugaban {asa Muhammadu Buhari, ya sa ake ganin cewa ita ma wannan dangantaka ta }ara taimakawa wajen ]aga kima da matsayin Sarkin da kuma Masarautar a idon duniya. Kamar yadda masarautar Borgu ta yi fice da suna a tarihi haka Sarkin Borgu Alhaji Haliru [antoro yake da matu}ar kima da matsayi a tsakanin sarakuna iyayen al’umma a }asar nan. Tsarin tafiyar da mulkinsa ya }ara tabbatar da shi a mtasayin shugaban al’umma abin koyi.

24. Aisha Buhari (Uwargidan Shugaban {asa) Hajiya Aisha Buhari fitila ce daga cikin matan da suka haska shekarar 2016 ba wai daga cikin matan yankin Arewa ko matan Nijeriya ba kawai, har ma da ]aukacin matan shugabannin wannan nahiya ta mu ta Afurka. Rawar da take takawa a matsayinta na uwargidan Shugaban {asa ta yi matu}ar tasiri wajen taimakawa shi kansa Shugaban {asa da kuma jam’iyyarsu ta APC ta fuskar sauke nauyin inganta rayuwar mata da ke cikin al}awuran da ta ]aukar musu a lokacin ya}in neman za~e. Yanzu haka tana taka gagarumar rawa wajen inganta rayuwar mata da yara }anana a }asar nan, shirin da ta runguma a matsayinta na uwargidan shugaban }asa domin ganin cewa mata da yara }anana ba a mayar da su saniyar ware ba ko kuma an ci da guminsu. Hajiya Aisha Buhari wadda ‘yar asalin Jihar Adamawa ce da ke yankin Arewa-Maso-Gabas, ta halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ta samu digirinta na farko a sha’anin mulki da kuma babban digiri na biyu akan harkokin }asashen waje daga Makarantar Horas da Jami’an Soji ta NDA da ke Kaduna. A matsayinta na Uwargidan Shugaban {asa Muhammadu Buhari, Aisha ta yi ho~~asa ainun wajen goya wa mijinta baya domin a samu sabuwar Nijeriya mai cike da tsaro da zaman lafiya da ingantaccen tattalin arziki da ayyukan yi ga mata da matasan }asar nan.

25. Hajiya Zainab Atiku Bagudu Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Atiku Bagudu na cikin jerin fitattun matan gwamnonin }asar nan da suka yi suna wajen tallafawa }o}arin da mazajensu ke yi na sauke nauyin inganta rayuwar jama’a da ke rataye a wuyansu. Zainab }wararriyar likita ce kuma likitan tuntu~a a fannin kula da lafiyar yara, ta ta~a aiki a matsayin likita kuma Babban Jami’ar Gudanarwar Asibitin Medicaid Radio-diagnostics, da ke Abuja. Haka ma ta ta~a zama likitar yara a asibitin Garki duk dai a Abuja. Kasancewarta uwa mai tsananin kishin ganin ci gaban al’umma, musamman inganta rayuwar mata da yara, Hajiya Zainab wacce ‘ya ce ga marigayi Marafan Sakkwato Alhaji Umaru Shinkafi, tana amfani da matsayinta na kasancewa uwargidan gwamna domin ganin cewa mata a jihar Kebbi sun kasance suna samun kulawa ga bu}atunsu. {wazonta da jajircewarta ne suka sanya a yau mata da yara a jihar Kebbi suka kasance ‘yan gata. Zainab ta taka rawar gani wajen tabbatar da samuwar harkokin yi ga mata ta hanyar koya musu sana’o’in hannu, haka ma ~angaren kula da kiwon lafiyar mata da }ananan yara a jihar yana samun kulawar musamman a dalilin kasancewarta masaniya kuma mai kishin wannan fannin. Za a iya kiran Hajiya Zainab Atiku Bagudu da baya goya marayu saboda irin yadda ta zama wata inuwa ga mata da }ananan yara a jihar ta Kebbi har ma ya kasance ta kafa wani tarihi abin koyi ga takwarorinta.

26. Farfesa Batulu Mukhtar (Mataimakiyar Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutse) Farfesa Fatima Batulu Mukhtar kallabi ce tsakanin rawuna da ta yi fice a duniyar ilimi, tana cikin }alilan na matan wannan yankin da suka yi katarin samun ilimi mai zurfi har zuwa na }oluluwar matakin ilimi na farfesa. Ita ce yanzu haka Mataimakiyar Shugabar sabuwar Jami’ar Tarayya ta Dutse da ke Jihar Jigawa. {wararriya ce kuma fitacciyar masaniya a fannin ilimin tsirrai. An haifi Batulu a Kano, a shekarar 1963, ta yi karatun furamare a makarantar furamare ta Shahuci da kuma furamaren kwana ta ‘yan mata ta Shekara. Ta samu takardar shaidar kammala karatun sakandare a shekarar 1980 daga Kwalejin Gwamnati ta ‘yan mata ta Dala da ke Kano. A shekarar 1984 ne Farfesa Fatima Batulu ta samu digirinta na farko daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a fannin nazarin tsirrai, ta kuma samu digirinta na biyu a wannan fanni daga Jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1994. A shekarar 2005 ne ta samu digirinta na dakta duk dai a wannan fanni. Ta soma aikin koyarwa a Jami’ar Bayero tun daga shekarar 1994 inda ta tattaka matattakalar koyarwa har zuwa lokacin da ta zama farfesa a shekarar 2010. A shekarar 2013 ne Jami’ar ta bayero ta bayar da ita aro ga sabuwar Jami’ar Northwest da Jihar ta kafa inda ta assasa tare da zamowa shugabar Tsangayar Kimiyya ta farko a Jami’ar. A shekarar 2015 kuma an za~e ta a matsayin Mataimakiyar Shugaban Jami’ar ta farko, inda daga nan ne aka na]a ta a matsayin Shugabar Jami’ar Tarayya ta Dutse. Farfesa Batulu ta kasance abin alfaharin al’ummar wannan yanki musamman mata ganin irin gudummawarta da kuma tarin nasarorin da take samu a duk wani mataki ko matsayi da ta samu kanta a kai.

27. Hadiza Bala Usman (Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta NPA) Sunan sabuwar Shugabar Hukumar kula da Tashoshin Ruwa ta {asa Hajiya Hadiza Bala Usman ba ba}on suna ba ne ga duk wanda ke bibiyar al’amura a }asar nan, domin fitacciya ce kuma shahararriyar ‘yar rajin }watar ‘yanci, mace mai kamar maza wadda za a iya cewa gwagwarmayarta na da sanannen tushe da asali, domin kuwa ‘ya ce a wurin marigayi Dakta Bala Usman wanda shi ma ba }ashin yadawa ba ne a fagen gwagwarmayar ya}i da rashin gaskiya, kan wannan za a iya cewa a nono ta sha ba haye ta yi ba. Ta yi suna wajen gwagwarmayar nuna rashin amincewa da tauye ‘yancin marasa }arfi, ta kasance ]aya daga cikin ]ai]aikun ‘yan gwagwarmaya mata da ake da su wa]anda suka kasance muryar wa]anda }arfin mulki ya hana a ji na su muryoyin. Tana cikin madugan matsin lamba akan hukumomin }asar nan na ganin an samu nasarar }wato yaran nan mata sama da 200 da aka sace daga Makarantar mata ta Chibok da ke Jihar Borno. Hasali ma tana sahun gaba na manyan shugabanni kuma jagororin ‘yan fafatukar ‘Bring Back Our Girls’ ta neman ganin an sako ‘yan matan na Chibok. Matsayin da take a kai na Shugabar Hukumar NPA da kuma irin kyakkyawan sauyi mai ma’ana da ta samar ga hukumar sun da]a tabbatar da Hajiya Hadiza Bala Usman a matsayin wata jakadiyar mata wadda ke samar da kyakkyawan wakilci ga mata tare da cire duk wani kokwanto akan shugancin mata da kuma tabbatar da cewa mata ma suna suka tara.

28. Hajiya Rabi Salisu (Shugabar Gidauniyar Tallafawa Rayuwar Mabu}ata ta ARFON) Gidauniyar samar da tallafi ga al’ummomi ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya kassara da ya}i da cin zarafin yara }anana wadda aka fi sani da Arrida Relief Foundation of Nigeria, ko kuma ARFON a ta}aice, Gidauniya ce da Hajiya Rabi Salisu ta assasa kuma take shugabanta. Wannan gidauniya ta kasance wata inuwa ga wa]annan al’ummomi musamman mata da yara }anana da rikicin ya mayar da su marayu tare da raba su da jin da]in rayuwarsu ta hanyar kange su daga samun damar gina rayuwar tsayuwa da }afafunsu. Hangen nesa tare da zurfin tunanin Hajiya Rabi Salisu wajen samar da wannan Gidauniyar tallafi ba }aramin tasiri ya ke yi ba wajen taimakawa rayuwar ire-iren wa]annan al’umomin. Yanzu haka wannan Gidauniya ta ARFON tana ]auke da nauyin kula da yara kusan 63 wa]anda suka }unshi marayu 47 da ta ]auko daga jihohin Borno da Yobe inda ta mayar da su a Jihar Kaduna inda take kula da su ta ~angaren abincinsu, suturarsu da kuma iliminsu. Shakka babu Hajiya Rabi Salisu ta kafa tarihi a fagen aikin jin}ai da taimakawa marasa galihu, ta shimfi]a wata turba da ya kamata a yi koyi da ita.

29. Hajiya Amina Muhammed (Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar [inkin Duniya) Sabuwar Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar [inkin Duniya kuma Ministar Muhalli mai barin gado ta }asa, Hajiya Amina Muhammed ‘yar asalin Jihar Gombe ce da aka haifa cikin shekarar 1961. Mace ce da ake matu}ar mutuntawa haka ma tana da matu}ar kima a idon duniya, Hajiya Amina ta kwashe sama da shekara 30 tana aiki akan fannonin da suka ji~inci samar da ci gaba a matakan gwamnatin da na kamfanoni daban-daban. Ta ta~a zama mai bayar da shawara ga tsohon shugaban }asa marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua da kuma Shugaban da ya shu]e Goodluck Jonathan akan Muradun {arni. Kasancewarta mace mai }wazo da haza}a wadda ta samu gogewa ainun saboda tsawon lokaci da ta kwashe tana hidima a matakan gwamnatin da kamfanoni da }ungiyoyi daban-daban, ya sa Hajiya Amina Muhammed ta kasance ]aya daga cikin mata mafi ]aukar hankalin jama’a a }asar nan. Har zuwa na]a ta akan mu}amin Ministar Kula da Muhalli da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a shekarar 2016, Hajiya Amina ta kasance Mashawarciya ta Musamman ga tsohon Babban Sakataren Majalisar [inkin Duniya Ban Ki-Moon, sanin gogewarta da kuma kaifin basirarta zai iya kasancewa dalili ko dalilan da suka sanya sabon Babban Sakataren Majalisar nuna bu}atarsa ga gwamnatin Nijeriya na ganin ta ba shi aron Hajiya Amina Muhammad domin ta kasance masa Mataimakiya. Kasancewar Hajiya Amina Muhammad a Majalisar [inkin Duniya, babban abin alfahari ne ga matan yankin Arewa, da matan Nijeriya, da na nahiyar Afurka da ma na duniya baki ]aya.

30. Wing Kwamanda Hajara Bashari Umaru Wing Kwamanda Hajara Bashari Umaru ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko, Musulma, ‘yan asalin yankin Arewa da ta ta~a kai ga wannan mu}amin a Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, mu}amin da ya yi daidai da na Laftanar a Rundunar Sojin Nijeriya. An haifi Wing Kwamanda Hajara a unguwar [orayi da ke Birnin Kano a ranar 19 ga watan Maris na shekarar 1964, ta yi karatun furamare a makarantar furamare ta Gwagwarwa da kuma furamaren St. Louis dake Kano da kuma Sakandaren St. Louis inda bayan ta kammala sai ta samu shiga makarantar koyon aikin jinya ta Kano, inda daga can ne ta samu ginuwar ra’ayin shiga aikin sojin sama inda ta shiga rundunar sojin sama ta }asa a shekarar 1986. Jarumar jami’ar rundunar sojin ta sama, ta yi aiki a rundunonin sojin da ke Ibadan da Kaduna da sauransu ta kuma halarci fagen daga a {asar Kongo. Wing Kwamanda Hajara ta }ara tabbatarwa duniya kirarin nan da ake yi cewa, 'duk abin da namiji zai yi, to mace za ta iya yin fiye da shi.'

31. Mubarak Ahmad (Mai Na’urar Hana Satar Mota) Mubarak Ahmad matashi ne da ya kafa muhimmin abin tarihi inda ya }era na'urar gano motar da aka sace. Matashin ya yi amfani da fasaharsa wajen tsara wannan na’urar wadda matu}ar aka ha]a ta a jikin mota, to za ta iya tona asirin ~arawon da ya saci motar da zaran ya kusanto jami'an tsaro. Ko bayan haka, wata hikimar na’urar da matashin ya }ir}ira ita ce yadda take taimakawa wajen kiran jami'an tsaro idan an samu hatsari. Mubarak na ]aya daga cikin matasa 'yan asalin Arewa da tauraruwarsu ta haska matu}a a shekarar 2016.

32. Abubakar Shu'aibu Nakurta (Mai {era Sassan Jikin Mutane) Abubakar Shu’aibu ]an asalin jihar Filato ne da ya shahara wajen }era sassan jikin mutane kamar hannuwa da }afafu ta hanyar kamfaninsa mai suna Naraguta Leather Works da ke garin Jos. Matashin fasihin ya da]a tabbatar da cewa akwai tarin basira da hikima a tattare da matasanmu wanda muddin za su samu dama tare da taimakon da ya kamata daga hukumomi, to kuwa su ma za su taimaka wajen ganin an rage ko kuma an magance matsalar yawaitar ci-ma-kwance a cikin al’umma.

33. Injiniya Ibrahim Nazifi Khalid (Mai Injimin Casar Shinkafa) A daidai lokacin da gwamnatin }asar nan ke }o}arin ganin Nijeriya ta kama hanyar wadata kanta da abinci ta hanyar }arfafa noman kayan abinci musamman shinkafa, Injiniya Iliyasu Nazifi Khalid ya kasance ]aya daga cikin matasan da suka shigo cikin wannan yun}urin na tabbatar da wannan mafarki. Injiniya Nazifi wanda ke da }warewa a fanninn injiniyancin sarrafa man fetur, ya ajiye aikinsa da Hukumar Kula da Rarraba Man Fetur ta DPR domin amfani da }wa}walwarsa wajen }era injin na casar shinkafa da zai iya cashewa tare da samar da tsaftatacciyar shinkafa har kimanin a}alla buhu 600 a duk rana. Wani abin mamaki da kuma birgewa game da wannan fasaha ta Injiniya Nazifi shi ne, wannan injin da ya }ir}ira ba ya amfani da lantarki ko kuma gas, al’amarin da ya sanya shi cikin }ir}ire-}ir}iren fasahar zamani masu cike da hikima da sau}in gudanarwa.

34. Muktar Adamu Fasaha (Ma}erin Mota Mai Amfani Da Hasken Rana) Mukhtar Adamu wanda ake yi wa la}abi da Mukhtar Fasaha matashi ne ]an asalin jihar Kano mai kimanin shekara 23 da haihuwa wanda ya yi nasarar }era wata mota wacce ba ruwanta da man fetur ko gas, maimakon hakan, motar tana amfani ne da hasken rana a matsayin makamashinta. Motar mai fa]in inci 40 da tsawon inci 72 tana da mazaunin mutum biyu duk da cewa za ta iya ]aukar mutane hu]u, a gwajin da ya yi, motar ta yi tafiyar sama da kilomita 1 ta hanyar amfani da hasken rana, al’amarin da ya sa motar ba ta yin kuka ballantana ta fitar da haya}i. Matashin wanda yanzu haka yaron shago ne a kasuwar Kantin Kwari ta Kano, ya yi amannar cewa zai iya inganta motar ta yadda za ta }ara inganci da kuma ]aukar hankali muddin ya samu irin taimaka da kuma goyon bayan da ya ke bu}ata ganin cewa ya shafe shekara biyu yana aikin samar da wannan da ya yi gwaji a kai. Mukhtar Fasaha ya yi karatunsa na furamare a makarantar furamare ta Maimuna Gwarzo a Kaduna, haka ma ya yi karatu a }aramar makarantar sakandaren Digital Science a Kaduna kafin ya koma Kano a shekarar 2010. Ko bayan wannan fasahar }ir}ira da ya yi, matashin yana gyaran rediyo da wayar salula, haka ma yana ha]a na’urar adana hasken lantarki ta inverter.

35. Amina Ali Nkeki (‘Yar Makarantar Chibok Ta Farko Da AKa Gano) Amina Ali Nkeki da ]aya daga cikin yaran nan ‘yan makaranta Sakandare ta Chibok su 276 da maya}an {ungiyar Boko Haram suka sace a shekarar 2014, wa]anda tun bayan da wasu 57 daga cikinsu suka samu gudowa daga inda ake tsare da su, ba a }ara jin ]uriyar sauran 219 ba fiye da shekara ]aya da sace su, sai a ranar 17 ga watan Mayun shekarar 2016 lokacin da matasa ‘yan sa kai masu taimakawa sojoji suka gano Amina Ali Nkeki wanda a lokacin ke tare da jinjirinta mai kimanin watanni hu]u. Amina ita ce yarinyar farko da aka ku~utar daga hannun Boko Haram daga cikin ‘yan matan da aka sace. Amina mai shekara 17 a lokacin da aka sace ta, ta fito ne daga garin Mbalala mai nisan kilomita 10 daga garin na Chibok, garin na Mbalala mai mutanen da suka kai kimanin 30,000 akasarin mazaunansa mabiya addinin Kirista ne sai dai ita Amina Nkeki ta fito daga gidan Musulmai kuma ita ce ta biyu daga cikin ‘ya’ya 13 na mahaifanta da suka rayu.

36. Laftanar Janar Tukur Buratai (Babban Hafsan Rundunar Sojin {asa) Laftanar Janar Tukur Buratai, na sahun gaba a cikin madugan fafatukar tabbatar da dawowar dawwamammen tsaro a }asar nan, shi ne Babban Hafsan Sojin Nijeriya, kuma jarumin hafsan soji mafi ]aukar hankalin jama’a a }asar nan. Kafin na]a shi a matsayin Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Janar Buratai wanda ya fito daga {aramar Hukumar Biu ta jihar Borno, shi ne Kwamandan sabuwar rundunar tabbatar da tsaro ta }asa da }asa ta MNJTF da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Arewa-Maso-Gabas. Jarumin soji ne da Rundunar Sojin Nijeriya ke matu}ar alfahari da shi a fannin }wazo da iya aiki, wannan na daga cikin abubuwan da gwamnati mai ci ta hango har ta na]a Janar Buratai a matsayin Babban Hafsan Sojin Nijeriya a watan Yulin shekarar 2015. [aukacin nasarorin da gwamnati ke ta samu na kassara {ungiyar Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci, ciki kuwa har da }wato Dajin Sambisa da rundunar Sojin Nijeriya ta yi tare da }wato dukkan wuraren da a baya suke }ar}ashin ikon Boko Haram, duk nasarori ne da za a danganta su da kyakkyawan shugabancin Babban Hafsan Sojin na }asa, wato Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.

37. Iya Bayis Mashal (AVM) Sadique Abubakar (Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama) Babu yadda za a yi bayanin nasarar mur}ushe matsalar ta’addancin {ungiyar Boko Haram ba tare da an ambato gagarumar gudummawar rundunar sojin sama ta Nijeriya ba, wadda Iya Bayis Mashal Sadique Abubakar ke jagoranta a matsayin Hafsan Sojin Sama na {asa. AVM Sadique Abubakar ]an asalin garin Azare ne da ke jihar Bauchi, hazi}in jami’in sojin Nijeriya ne da ya kwashe tsawon lokaci yana yi wa }asar nan hidima, tare da ha]in gwiwar rundunarsa ta sojin sama ne aka samun nasarar cin }arfin {ungiyar Boko Haram domin kuwa rundunar na sahun gaba wajen dukkan tsare-tsaren da aka tsara kana aka aiwatar da ganin bayan {ungiyar ciki kuwa har da }wato Dajin Sambisa. Sadique Abubakar ya ri}a mu}amai daban-daban a Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya wa]anda suka ha]a da Kwamandan Cibiyar Sojin Sama dake Maiduguri da kuma Mu}addashin Kwamandan Sojin Sama na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta NEMA. Kafin na]a shi a matsayin Hafsan Sojin Sama na 20 na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, AVM Sadique Babban Jami’in gudanar da mulki ne a Hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta {asa.

38. Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman (Daraktan Hul]a da Jama’a na Rundunar Sojin) Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman, yanzu kuma Daraktan Hul]a da Jama’a na Rundunar Sojin Nijeriya fitacce ne a cikin jami’an tsaron Nijeriya da sunansu ya yi fice a gwagwarmayar ya}ar ayyukan ta’addanci a }asar nan. Birgediya-Janar Usman ya kasance wata madogarar samun sahihai, ingantattu kuma }wararan bayanai dangane da fafatawar da Rundunar Sojin Nijeriya ke yi da maya}an Boko Haram. Gabanin na]insa a matsayin Kakakin Rundunar Soji, ya ta~a ri}a mu}amin Mataimakin Daraktan Hul]a da Jama’a na Rundunar Sojin Nijeriya ta 7 da ke yankin Arewa-maso-Gabas. A watan Janairun wannan shekarar ne Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da na]insa a matsayin Daraktanta na hul]a da jama’a bayan }arin girma da aka yi masa daga mu}amin Kanal zuwa Birgediya-Janar.

39. Alhaji Muhammad Aliko Dangote Alhaji Aliko [angote, shugaban rukunin kamfunnan [angote, shi ne ]an Afurka kuma ba}ar fata mafi tarin arziki a duniya. Ya ciri tuta ainun a fannin bun}asa tattalin arziki a Nijeriya da kuma Nahiyar Afurka. Ba wani ]an kasuwa da ya taka rawar da za aiya kwatantawa da wadda ya taka a fannin samar da masana’antu ya ayyukan yi ga dubban jama’a a shekarar 2016. [angote ya bayar da gagarumar gudummawa ga bun}asuwar tattalin arziki, ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga dubban jama’a, giwa ne a fannin jin}ayi da tausayin jama’a kuwa, abin koyi ne ga sauran masu hannu da shuni. Harkokin kasuwancinsa sun da]e da fa]a]a zuwa sassa daban-daban na nahiyoyin Afurka da Asiya, inda yanzu haka yake gudanar da harkokin kasuwancinsa a }asashen Afurka kimanin 18.

40. Alhaji Auwalu Abdullahi Rano (A A Rano) Alhaji Auwalu Abdullahi Rano matashin ]an kasuwa ne da ke cikin kakar ha~aka da bun}asa harkokin kasuwanci tun ma dai ba ~angaren hada-hadar man fetur da gas ba. Shi ne Shugaban Kamfanin A. A Rano, sunan da ya yi fice a ciki da wajen }asar nan a farfajiyar harkokin kasuwanci. Tun a shekarar 1990 ne dai Alhaji Auwalu Abdullahi ya samar da wannan Kamfani na A.A Rano, an kuma mayar da shi zuwa ha]a]]en kamfani a shekarar 2001. Kamfanin dai ya shahara ne a harkar hada-hadar man fetur da gas da kuma man kalanzir. Ya zuwa yanzu ba wani lungu ko sa}o da manyan biranen jihohin Nijeriya da rassan kamfanin A.A Rano ba su kai ba. Matashin ]an kasuwar ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da harkokin yi ga ]aruruwan matasa wa]anda a yau ke samun abin sakawa aljihu da ma na ajiyewa domin sauran bu}atun rayuwa ta sanadiyar harkokin kasuwancinsa.

41. Fasto Yohanna Buru Fasto Yohanna Y. Buru, limamin addinin Kirista ne da ke zaune a jihar Kaduna, fitaccen limamin addinin Kirista ne kuma mai wa’azi da ya da]e yana gwagwarmayar ganin an samu fahimtar juna tsakanin mabiya addinan Musulunci da na Kirista, akan haka ne ya assasa tare da samar da wata }ungiyar farfa]o da zaman lafiya da sasantawa tsakanin addinai ko }abilu, wadda a turance ake kira da Peace Revival and Reconciliation Foundation. Da wannan }ungiyar ne Fasto Buru ya yi amfani a lokuta da dama domin ganin an samu ha]a kai da kuma samar da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai musamman tsakanin mabiya addinin Musulunci da mabiya addinin Kirista. Gudummawarsa ta wannan fuska a ciki da wajen Jihar Kaduna da kuma }o}arin samar da wanzajjen zaman lafiya a tsakanin mabambantan }abilu a sassan Jihar Kaduna da dama sun sanya ana yi wa Fasto Buru duban jakadan samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Fasto Buru na da matu}ar kima da mutunci a tsakanin al’umma wannan ne ya sa ake yawan samun musanyar ziyarce-ziyarce tsakaninsa da wasu sassan mabiya addinin Musulunci musamman a lokutan bukukuwa da sauran hidimomin addini.

42. Ahmed Musa (Shahararren [an Wasan {wallon {afa) A fagen murza tamola ba wani matashin ]an wasa da a yau zai shiga gaban Ahmed Musa, matasahin ]an wasan }wallon }afa da ya yi fice a ciki da wajen }asar nan wajen taka leda. Ahmed Musa ya kafa tarihin zama ]an wasan Nijeriya na farko da ya ta~a cin }wallo fiye da ]aya a duk wani wasan cin kofin }wallon }afa na duniya bayan da ya zura }wallaye biyu a ragar ‘yan wasan }asar Ajantina a gasar cin kofin duniya na shekarar 2014. Matashin ]an wasan da aka haifa a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 1992 yana cikin manyan ‘yan wasan }wallon }afa na Nijeriya kuma ]aya daga cikin ‘yan wasan gaba da kulob ]in wasan }wallon Premier na Leicester City ke ji da shi kamar }urjin gwiwa. Ya soma buga wasanninsa ne da kulob ]in JUTH FC na jihar Filato da Kano Pillars, har ma ya ta~a zama ]an wasa mafi zura }wallaye raga a wasannin Premier na kulob ]in }wallon }afa a Nijeriya. Ahmad Musa na cikin jerin ‘yan wasan }wallon }afa na duniya su 100, kuma ]aya daga cikin ‘yan wasa 10 mafi }wazo na Nijeriya. Ya ta~a lashe kyautar ]an wasan shekara na gidan talabijin AIT a shekarar 2011. Shi ne ]an wasa na biyar a jerin ‘yan wasan da suka fi zura }wallaye raga a gasar premier ta Russian Premier League ta shekarar 2015/2016

43. AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WA{A) Aminu Ala fasihin mawa}in Hausa ne da sunansa ya yi tambari a ciki da wajen }asar nan a fannin fa]akarwa da ilmantarwa da kuma ni]ashantar da jama’a. Yana sahun gaba a cikin mutanen da suka bayar da gagarumar gudummawa ga ha~aka Adabin Hausa. Hazi}in mawa}i ne kuma shahararren marubuci mai tarin hikima da basirar sarrafa zance da kalamai, shi ya sa wa}o}insa suka kasance masu jan hankali da tagomashi a wurin jama’a. Haifaffen unguwar Tudun Murtala da ke cikin birnin Kano, an haifi Aminu Ala a cikin shekarar 1973, ya yi karatunsa na furamare a Tudun Murtala daga shekarar 1980 zuwa 1986 da makarantar sakandare ta Dakata Kawaji daga shekarar 1986 zuwa 1992. Aminu Ala yana da mallakar takardar shaidar difiloma a fannin fasahar }ir}irar zane wato Arts and Design. Tun a shekarar 1992 ya shigo gonar rubuce-rubuce, haka ma ya da]e yana rera wa}o}i amma dai sai a wuraren shekarar 2003 wa}o}in nasa suka soma shiga duniya. Yanzu haka yana da mallakar kamfanin buga wa}o}i mai suna Ala global.

44. MALAM YAHAYA MAKAHO (Sha’irin Makaho Mai Hikima) Malam Yahaya Makaho na daga cikin ]ai]aikun masu ]auke da wata lalura ta nakasa da suka barranta daga zama ‘yan Allah-ba-ku-mu-samu, suka du}afa ga neman abin da za su gina rayuwarsu har ma su gina wasu. Malam Yahaya Makaho, ajiyar Allah ce, ganin cewa duk da kasancewa bai da idanu, Allah ya ba shi kaifin basira da ilimi inda yake rera rubutattun wa}o}in Hausa masu cike da hikima wa]anda kuma ke ]auke da sa}o zuwa ga jama’a. Yadda Malam Yahaya ke cikakken amfani da fasaha da basirar da Allah ya ba shi maimakon yawon barace- barace da masu lalura irin ta sa ke yi, ya da]a jaddada zancen da ake yi cewa, a cikin duk wata tawaya to akwai baiwa da hikima.

45. Ja’afar Ja’afar Ga duk mai bibiyar kafafen sadarwa musamman na zamani wa]anda ke gudana a duniyar gizo, sunan Ja’afar Ja’far ba ba}on suna ba ne. Ja’afar }wararren marubuci ne, manazarci, edita kuma hazi}in mai sharhi akan al’amuran yau da kullum. Yana da digiri na ]aya da na biyu akan harkokin ya]a labarai da ya samu daga Jami’ar Bayero ta Kano. Haka ma yana da takardar shaidar difiloma a fannin hul]a da jama’a daga makarantar London School of Public Relations dake }asar Ingila. Ya ta~a aiki a matsayin mai farauto labaru da kamfanin buga jaridu na Daily Trust daga shekarar 2007 zuwa 2011. Haka ma ya zama mataimakin musamman ga gwamnan jihar Kano a fannin watsa labarai daga shekarar 2011 zuwa 2015. Ko baya ga wannan mu}ami Ja’afar ya yi aiki a matsayin Edita da kafar ya]a labarai a duniyar intanet ta Premium Times. {warewar da Ja'afar Ja'afar yake da ita ta sanya ya }i}iro da kafar ya]a labari ta intanet mai suna, www.dailynigerian.com, inda yake yawan buga labari zafafa da ]imi-]iminsu.

46. Bashir Ahmad (Mataimakin Musamman Ga Shugaban {asa) Za a iya kiransa da kakakin gwamnatin Shugaban {asa Muhammadu Buhari a kafafen sadarwar duniyar intanet kasancewarsa Mataimaki na musamman ga Shugaban {asa a fannin kafafen sadarwa na nazami. Bashir Ahmad matashin ]an jarida ne kuma hazi}in marubuci wanda ke gudanar da aiki cikin }warewa da kaifin basira. Matashin wanda ]an asalin jihar Kano ne, yana da mallakar digiri a fannin aikin watsa labarai daga Jami’ar Bayero. Gogagge ne a wannan fage wanda ya ta~a aiki da gidajen Jaridu kamar Rariya da Leadership da kuma Mujallar Muryar Arewa wadda ya kasance babban wakilinta a jihar Kano. Bashir Ahmad yana aiki tu}uru wajen tafiyar da wannan jan aiki da aka ]ora masa na mai taimakawa shugaban }asa. Shafukan sadarwarsa da ke dandalin sada zumunta na Facebook da na Twitter sun kasance wata male}ar le}awa domin samun sahihan bayanai da labarai game da fadar Shugaban {asa da kuma shi kansa Shugaban.

47. Nasir El-Rufa'i Malam Nasiru El-Rufa'i ya cancanci zama ]aya daga cikin fitattun 'Yan Arewa 100 da suka yi fice wajen bun}asa rayuwar al'umma a shekarar 2016 da ta gabata. A matsayinsa na Gwamnan Jihar Kaduna yana fa]i tashin shimfi]a ayyukan raya jiha da ci gaban al'umma a kowane fannin na rayuwar al'umma a kuma lungu da sa}on Birnin na Gwamna. Shirinsa na agajin gaggawa a fannin ilimi da zummar farfa]o da sha'anin ilimi da ya ta~ar~are a jihar abin yabawa ne ainun kamar kuma yadda ya himmatu wajen bun}asa sha'anin aikin gona tare da tallafawa manoman rani da na damina, baya ga kyautata walwala da jin da]in ma'aikatan jiharsa da kuma uwa uba yun}urin da Gwamnatinsa ke yi wajen shawo kan ayyukan ta'addanci da ke gudana a Kudancin Kaduna. Duka baya ga wannan ga kuma shirin musamman na ciyar da ]aliban makarantun furamare da ya ~ullo da shi da kuma sau}a}awa wajen biyan ku]in karatu a makarantun Sakandare a fa]in jihar baki ]aya.

48. Abubakar Atiku Bagudu Gwamna Bagudu yana daga cikin Gwamnonin Arewa da suka yi fice a shekarar 2016 musamman a wannan lokacin da Nijeriya da al'ummarta suka ]aura ]amarar noma wadataccen abinci a cikin }asa tare da rage dogaro da abincin da ake shigowa da shi. Shirin noman shinkafa da alkama da Shugaba Muhammadu Buhari ya }addamar a Birnin Kebbi da ha]in guiwar Babban Bankin Nijeriya ya }ara haskaka jihar Kabi tare da }ara ]aukaka siyasar Gwamna Bagudu a matsayinsa na jagoran tabbatar da noman shinkafa a Kebbi. Haka ma }awancen Jihar Kebbi da Gwamnatin Jihar Legas wajen sarrafa shinkafa da aka fi sani da LakeRice wani ci gaba ne da wasu jihohi suka ]auki haramar koyi a kai. Duka baya ga wannan, Gwamna Bagudu bai yi }asa a gwiwa ba wajen shayar da Kabawa romon mulkin Dimokura]iyya ta hanyar gudanar da ayyukan da suka ta~a rayuwar talaka ta fuskar kiwon lafiya da samar da ruwan sha da shimfi]a hanyoyi da biyan albashi kan kari da kyautata tsarin aikin Gwamnati. Haka ma a yayin da al'ummar Nijeriya ke ci gaba da rayuwa a cikin tsananin duhu da ya mamaye ko'ina; Jihar Kebbi ta tserewa tsara domin kuwa ta samu wadatacciyar hasken wutar lantarki a Birni da Kewaye.

49. Aminu Waziri Tambuwal Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samarwa kansa suna a matsayin nagartaccen adalin shugaba mai kamanta gaskiya da adalci kamar yadda Sakkwatawa da dama suke bayyanawa a bisa ga salon mulkinsa na yi wa jihar Sakkwato zobe da ayyukan ci gaban al'umma tare da fitowa da shiraruwa masu amfani da alfanu ga al'ummar Jihar. Tarihi ya adana shiraruwan Gwamna Tambuwal kan ]aukin gaggawa a fannin ilimi da shirin bun}asa aikin noma da kiwo da shirin ba sani ba sabo ga duk ma'aikacin da aka samu yana wasa da zuwa wajen aiki da kuma shirin koyawa matasa sana'o'i a matsayin shiraruwan da suka ]aga hasken Gwamnatinsa. Tambuwal ya yi zarra hatta a cikin takwarorinsa Gwamnoni domin a yayin da Jihohi da dama ma'aikata ke bin Gwamnati bashin albashin watanni a dalilin ta~ar~arewar tattalin arzikin }asa, a Sakkwato ma'aikata sai Sam Barka suke yi domin babu watan da aka kasa samun albashi cikin lokaci, ballantana har ma'aikata su bi bashi. Bugu da }ari Gwamnatin Tambuwal ce ta farko a Nijeriya da ta sanyawa dokar tilastawa 'ya'ya mata karatu hannu tare da bayar da cikakken 'yancin gashin kai ga fannin shari'a wa]anda duka suke a matsayin ma'aunin da ke nuna jajircewar Tambuwal wajen raya Jihar Sakkwato.

50. Yusuf Datti Baba-Ahmed A yayin da al'ummar Kudancin }asa suka yi wa yankin Arewa fintinkau a fannin ilimi musamman ta hanyar kafa jami'o'i masu zaman kansu; Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya nuna a fili cewar yana kishin ci gaban Arewa da al'ummarta ta hanyar kafa Jami'ar Baze da ke Abuja wadda tuni ta samarwa kanta suna a matsayin fitacciyar jami'ar da ta samu shaidar }warewa da gogewa wajen ilmantar da al’umma. A yau Jami'ar Baze ta zama zakaran gwajin dafi kuma fagen neman ingantaccen ilimi da ya]a shi da Arewa ke bugun gaba. Kenan Sanata Datti Baba Ahmad ya cancanci zama cikin fitattun mutanen Arewa 100 da suka taka rawa a baya, suka taka a shekarar 2016, kuma za su ci gaba da takawa a gaba.

51. Tsohon Mataimakin Shugaban }asa, Atiku Abubakar mashahuri ne a fagen siyasar Nijeriya. Ya himmatu }warai ainun wajen ganin Dimokura]iyyar Nijeriya ta ]ore tare da zama kan }afafun ta. Tarihi ba zai manta da yadda Turakin Adamawa ya }alubalanci Obasanjo a yayin da ya bu}aci zarcewa saman mulki a wa'adi na uku ba. Bugu da }ari ba za a manta da gagarumar gudunmuwar da Atiku ya bayar wajen samun nasarar Shugaba Muhammadu Buhari da kuma yadda a yau yake bayyana ra'ayinsa da hangen sa kan yadda ya kamata a inganta mulki tare da fita daga }angin ta~ar~arewar tattalin arzikin }asa. A yanzu haka Atiku ya himmatu wajen ganin 'yan gudun hijira sun samu kyakkyawar makoma ta hanyar tallafin da yake ba su. Baya ga wannan a shekarar 2016 ne babban jigon ]an siyasar ya }arawa ma'aikatan jami'arsa ta American University, Yola albashi kashi 100 bisa 100 da zummar inganta jin da]in su a daidai lokacin da kayan amfanin yau da kullum suka yi tashin gwauron zabo.

52. Bindow Jibrilla Gabanin hawan mulkin Sanata Muhammad Umar Bindow Jibrilla a watan Mayun shekarar 2015, al'ummar jihar Adamawa sun yi }orafin bahagon salon tafiyar da mulkin Gwamnonin da suka shugabanci jihar tun daga shekarar 1999 ta yadda a yau aka shaidi wayewar sabuwar safiya a haujin sauke nauyin da al'ummar jihar suka ]orawa Gwamnan. A yau an shaidi yadda Gwamnan ya jajirce wajen tayar da koma]ar jihar Adamawa. Ayyukan sa na inganta kiwon lafiya da gina asibitoci da samar da magani da kayan aiki da kuma }wararrun ma'aikata abin yabawa ne ainun kamar yadda ya kutsa kai a Birni da Karkara domin ganin al'ummarsa sun amfana da ilimi mai inganci da kuma ruwan sha wadatattu kuma masu tsabta. Haka ma a mulkin Gwamna Bindow an shaidi aikin samar da muhallin gidaje 300 domin amfanin 'ya'yan jihar kamar kuma yadda Gwamnatin ta biya albashin watanni da dama da ma'aikatan jihar ke bin bashi ga tsohuwar Gwamnatin da ta gabata.

53. Aminu Bello Masari Jihar Katsina na ]aya daga cikin jihohin da al'umma suka tabbatar da cewar an samu canji a bisa ga yadda jagoran Jihar ya ]aura ]amarar baiwa mara]a kunya ta hanyar gudanar da mulkin da al'ummar Jihar ke yabawa a yau. Ayyukan alheri da Gwamna Aminu Bello Masari ke aiwatarwa Katsina a fili suke a mabambantan fannonin bun}asa lafiyar al'umma da inganta ilimin su da samar da ruwan sha da shimfi]a hanyoyi da sabunta wasu da dama baya ga kula da ma'aikatan jiha da na }ananan Hukumomi da sauransu da dama wa]anda ke nuni da cewar Tsohon Shugaban na Majalisar Wakilai ta Shida ya baza }aimi wajen kai ta Dikko ]akin Kara a tudun mun tsira.

54. Rabi'u Rikadawa Idan a na maganar fitacce kuma shahararren ]an wasan Hausa wanda wasanninsa suka }ayatar da masu kallo a shekarar 2016 wajibi ne a ambato Rabi'u Rikadawa a sahun farko. A so shi, ko a }i shi, Rikadawa wanda aka fara ]orawa kamara a wasannin talbijin a shekarar 1986 fitaccen ]an wasa ne wanda ke da hikima da fasahar sace zukatan 'yan kallo cikin ruwan sanyi. Fina-finan da ya fito cikin su a 2016 kamar Baya da }ura da Akasi da Zinaru da Illar Bariki da kuma Mati da Lado duka sun nuna yadda Rikadawa ke amfani da damar da Allah ya ba shi wajen fa]akarwa da ilmantarwa da nisha]antar da al'umma a }oluluwar mataki na }wararru. Bugu da }ari ]an wasan wanda ake kira da 'Dila' yana cikin manyan jaruman Kannywood wa]anda a ciki da wajen farfajiyar wasan Hausa ake girmamawa a matsayinsa na mutum mai dattako da sanin ya kamata wanda ke fitowa a matsayin mahaifi. Fim ]in Sarauniya na daga cikin manyan sababbin Fina-Finansa da za su haska a wannan shekarar ta 2017 ta yadda za a }ara tabbatar da cewar Rikadawa ba }yalle ba ne, babban bargo ne.

55. Sadik Sani Sadi} Sadik Sani Sadi} fitaccen jarumi ne da daraktoci ke rububi saboda yana amfani da hikima, }warewa da gogewa wajen jan zaren labari ya tafi yadda ake so. Yana da tarin masoya a duk inda ake kallon fina-finan Kannywood wa]anda zukatansu kan yi fari a duk lokacin da aka hasko shi a akwatin talbijin. Fina-Finansa kama daga [an-Marayan Zaki da Bayan Duhu da Mati Da Lado da Wani Gari da Hanyar Kano da kuma Ali Ya Ga Ali, sun nuna lallai za a ci gaba da damawa da jarumin wanda ya samu nasarar zama Gwarzon Jarumin - Jarumai a gasar MTN/Kannywood Award a karo biyu a jere tare da samun lambobin karramawa daban- daban a bisa ga irin siffofin da yake takawa a matsayin jarumi ko matallafin jarumi.

56. Hafsat Idris Hafsat Idris ita ce jaruma mafi samun kar~uwa a masana’antar Kannywood a shekarar 2016. Zaman Hafsat a matsayin sabuwar jaruma bai hana mata nunawa duniya irin baiwar da Allah ya yi mata ta }ayatar da masu kallo ba. |arauniya, 'Yar Fim, Al}ibla, Furuci, Haske Biyu da kuma Buki-Buduri fina-finai ne da ta fito wa]anda suka ]aga darajarta tare da kaita matsayin gwana ta gwanaye. Jarumar wadda furudososhi ke ya yi, ta kan dace da labaran da ake ]ora ta wanda hakan ya nuna za ta ci kasuwa sosai a masana’antar.

57. Inuwa Abdul}adir Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin Arewa Maso Yamma, Barista Inuwa Abdul}adir yana daga cikin 'yan siyasar da suka zamo abin ambaton al'ummar }asa a shekarar da ta gabata. Sunansa ya }ara fita a bisa ga matsayin ofishin sa wajen sasanta rikicin jam'iyyar APC musamman a jihohin Kaduna da Kano. Inuwa Abdul}adir wanda ya ri}e mu}amin Ministan Matasa a Gwamnatin Jonathan yana sahun gaba wajen bayar da gagarumar gudunmuwa ga samun nasarar APC a matakin }asa baki ]aya.

58. Abdullahi Mukhtar Ba za a ta~a mantawa da shugabancin Abdullahi Mukhtar a Hukumar Kula Da Jin Da]in Alhazai ta }asa (NAHCOM) ba, musamman yadda ya jagoranci fitowa da tsare-tsare da shiraruwa masu alfanu ga Alhazai wa]anda suka sau}a}a masu gudanar da aikin Hajji a }asa mai tsalki. A matsayinsa na Shugaba ya samu nasarori da dama wa]anda su kansu Hukumomin Alhazai a Jihohi ke bayyanawa da cewar shugabancinsa abin koyi ne da kwatance, wanda Alhazai maza da mata ke yabawa a kai.

59. Sanata Ali Ndume Sanata Ali Ndume fitacce ne a Majalisar Tarayya. Ya fara jan zaren wakilci a Majalisar Wakilai gabanin ya samu ci gaban zama Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa ta Takwas. Sanata Ndume yana sahun gaba na Sanatocin da suka taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Sanata Bukola Saraki a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa a Yuni 2015. Sanata Ndume ya }ara bayyanar da kansa a matsayin nagartaccen ]an siyasa a yayin da Majalisar Dattawa ta cire shi daga kan kujerarsa ta Jagoran Majalisa lamarin da ya fito fili ya bayyana cewar an yi awon gaba da shi ne saboda ya bayyana goyon bayansa ga tantance Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC tare da bayyana kura-kuran da Majalisar Dattawa ta tafka na }in amincewa da bu}atar Shugaban }asa ta tantance Magu.

60. Lawal Daura Hukumar le}en asiri ta }asa DSS a }ar}ashin shugabancin Lawal Daura ta jajirce wajen gudanar da ayyukan ba- sani-ba-sabo ga duk wanda ya taka doka, to tabbas doka za ta yi aiki kansa matakin da a yau ya taimaka wajen dawo da kima da martabar Hukumar a idanun al'umma da }asashen duniya baki]aya. A shekarun baya masu ri}e da madafun iko kan yi katsalandan wajen gudanar da ayyukan SSS amma kuma a yau lamarin ya canza domin Daura ya samu cikakken 'yancin tafiyar da ayyukan sa yadda ya kamata wanda hakan ya ba shi damar sarawa ko babu ga~a a duk inda bu}atar hakan ta kama.

61. Garba Shehu Garba Shehu ba ya bu}atar gabatarwa. Jama'a sun san shi a matsayin Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, yana kuma gudanar da aikin da aka ]ora masa a matsayin Mataimaki na Musamman a Aikin Ya]a Labarai yadda ya kamata domin kuwa bai ta~a yin }asa a guiwa ba wajen ya]a manufofi da }udurorin Gwamnatin Muhammadu Buhari. Bugu da }ari Garba Shehu ya nunawa duniya cewar aikin zama Kakakin Fadar Mulki aiki ne na }wararru wa]anda suka ji gishiri tare da la}antar dabaru da hanyoyin wayar da kan al'umma da kuma kariyar manufofin Gwamnati a inda ke bu}atar hakan.

62. Kanar Hameed Ali Shugaban Hukumar Kwastam Ta Nijeriya, Kanar Hameed Ibrahim Ali babban jigo ne a tafiyar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari domin kuwa Gwamnatin Tarayya ta karkatar da hankalin ta ga Hukumar Kwastam musamman a daidai lokacin da farashin albarkatun man fetur ya fa]i }asa a kasuwannin duniya. A Shekarar da ta gabata ne Hukumar Kwastam ta haramta shigowa da abinci da kuma dakatar da shigowa da motoci ta bakin bodojin }asa tare da umurtar a ri}a shigowa da mota a Legas ta bakin ruwa matakin da Hukumar ta ce ta ]auka da kyakkyawar manufar ha~aka tattalin arzikin Nijeriya. Bugu da }ari a shekarar 2016 ne Hukumar Kwastam ta samu tattara ku]a]en haraji har naira bilyan 898 kamar yadda Hukumar ta bayyana a watan Janairu 2017. Baya ga wannan tuni Shugaban Hukumar ya ]aura ]amarar magance cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da bin doka da oda a Hukumar wadda shugaban ke fafatukar ganin ya dawo da kima da martabar ta a idanun al'umma.

63. Cif Audu Ogbeh [an siyasa ne wanda ya jima yana iyo da nin}aya a farfajiyar siyasa tun a Jamhuriya ta biyu zuwa yau da yake matsayin jagoran 'yan siyasa da dama. Ogbeh wanda ya ri}e mu}amin Shugabancin Jam'iyyar PDP a zamanin mulkin Obasanjo a yanzu haka a matsayinsa na Ministan Aikin Gona ya himmatu wajen ganin al'ummar Nijeriya sun rungumi noma da zummar wadata }asa da abinci tare da bankwana da abincin da ake shigowa da shi daga wajen }asa. Shiraruwan da Ogbeh ya fito da su ingantattu ne wa]anda nan da can lokaci za a fara cin moriyar su.

64. Hamza Al- Mustapha Babban Jami'in Tsaron Lafiyar Shugaba Janar , Manjo Hamza Al-Mustapha yana daga cikin sojojin da Nijeriya ba za ta yi saurin mantawa da su ba. Al-Mustapha wanda ya kwashe tsayin shekaru ]aure a Kurkuku a Legas a kan zargin kisan Kudirat Abiola, uwar gidan Chief Moshood MKO Abiola a yanzu haka Kotun {oli ta baiwa Gwamnatin Jihar Lagas damar ]aukaka }ara. Manjo Al-Mustapha shi ne dogarin Shugaban }asa mafi }arfin iko da aka ta~a yi a Nijeriya. Haka ma ya samarwa kansa suna a matsayin jami'in soji mai }wazo, himma da cika aiki. Almustapha na daga cikin jerin wa]anda ke bayar da gagarumar gudunmuwa wajen wantsuwar zaman lafiya da ya}i da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

65. Halima [angote Halima [angote babbar 'yar Attajiri mafi ku]i a Nahiyar Afurka Aliko [angote tana kan gaba wajen samun nasara da ]aukakar Rukunin Kamfanonin [angote. Halima wadda ita ce Mataimakiya ta Musamman ga Shugaba kuma Babban Jami'in Gudanarwa na Kamfanin [angote haka ma tana cikin kwamitin amintattu na Gidauniyar [angote wadda aka fi sani da [angote Foundation. Halima wadda ke da digiri na biyu a fannin kasuwanci da kuma digiri na ]aya a fannin tallata haja ta zama kallabi tsakanin rawuna ta hanyar himma da }wazo a sha'anin kasuwanci da fa]a]a ayukkan kamfanin [angote.

66. Farfesa Umar Garba [anbatta Farfesa [anbatta shi ne Mataimakin Shugaban Hukumar Kula Da Kamfanonin Sadarwa kuma Babban Jami'in Gudanarwa na NCC. Shigarsa ofis zuwa yau ya jagoranci canza fasali da salon aikin NCC ta hanyar samar da canja akalar yadda Kamfanonin Sadarwa ke cin karensu babu babbaka ta hanyar kawar da kai ga biyan Gwamnati harajin da ya kamata. A }ar}ashin shugagancinsa ne Hukumarsa ta ci kamfanin sadarwa na MTN tarar naira bilyan 330 a matsayin ku]in tarar da kamfanin ya kawar da kai ga biyan Gwamnatin Tarayya. Haka ma [anbatta wanda ya samu lambar girma ta Babban Jami'in Sadarwa na 2016 ya fito da hanyoyi da dama da Kamfunan Sadarwa za su yi amfani wajen inganta ayyukan su.

67. Fatima Kyari Muhammad Fatima Kyari ta yi zarra a matsayin mai rajin samar da zaman lafiya da ci gaba, aikin da take yi a jiya da yau. Tana kuma ]aya daga cikin wa]anda suka assasa tare da jagorantar shirin nan na LikeMinds Project. Ta kuma kwashe shekaru tana aiki da {ungiyar {asashen Afurka ta ECOWAS. A watan Janairu ne ta fafata za~en neman zama kan kujerar Kwamishinar {ungiyar Tarayyar Afurka (African Union) kan samar da zaman lafiya da tsaro a Addis Ababa. Duk da yake ba ta samu nasara a za~en da Nijeriya da ECOWAS suka tura ta ba, amma ta nuna qwazo da bajinta, ta kuma taka wata matattakala wadda mata da yawa ba su taka ba. Fatima ta bayyana cewar Nijeriya ta na gaba wajen samar da zaman lafiya a Afurka don haka ta yi al}awarin idan ta samu nasara za ta shiga cikin rigar Nijeriya domin magance matsalolin rashin zaman lafiya da savani da ke addabar yankin.

68. Abubakar Malami SAN Ministan Shari'a na Tarayyar Nijeriya, Abubakar Malami SAN }wararre ne wanda ya san ciki da wajen aikin shari'a tare da amfani da gogewarsa da sanin makamar aiki wajen bun}asa aikin shari'a ta hanyar fitowa da tsare-tsare masu ma'ana da alfanu. Fitaccen jigon na jam'iyyar APC daga Jihar Kebbi, Abubakar Malami yana sahun farko a Gwamnatin Muhammadu Buhari wa]anda ke bayar da cikakken goyon baya a shirin Gwamnatin Tarayya na ya}i da cin hanci da rashawa. Ho~~asar da Ministan ke yi domin ganin an kar~o ku]a]en da ake zargin an sace a Gwamnatin da ta gabata tare da hukunta wa]anda ke da hannu da uwa uba tsarkake aikin shari'a tare da tabbatar da ingantaccen tsari duka abubuwan yabawa ne wa]anda ya zama tilas a jinjinawa Ministan kan aiki tu}uru da sadaukar da kai ga duk wani aiki da ya sanya a gaba.

69. Ibrahim Wakkala Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala Muhammad babban jigo ne a siyasar Jihar Zamfara a jiya da yau. An dama da shi a matsayin Kwamishinan Lamurran Addini a Gwamnatin Ahmad Sani Yariman Bakura, ana kuma damawa da shi a yau a matsayin mutum mafi daraja ta biyu a jihar wadda ke da taken 'Addininmu, Al'ummarmu.' Wakkala a matsayin Mataimakin Gwamnan ya bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci gaban al’umma da siyasar Jihar Zamfara a Gwamnatance da kuma a }ar}ashin aljihunsa ba tare da }osawa ko gajiya ba ta yadda a yau al'ummar Jihar da dama ke yi masa fata tagari lamiri.

70. Zainab Adamu Bulkacuwa Idan a na maganar aikin shari'a a Nijeriya, Zainab Bulkacuwa ba }yalle ba ce babban bargo ce. Ta ciri tuta ta kuma samarwa kanta suna a fannin da ta fi iyawa, wayo da la}anta. Bulkacuwa wadda ta zo duniya a shekarar 1950, ta fara aikin lauya a shekarar 1976, ta kuma fara aiki a Kotun ]aukaka }ara a shekarar 1998 tare da kaiwa }ololuwar zama Shugabar Kotun ]aukaka }ara ta Nijeriya a shekarar 2014, mu}amin da take ri}e da shi zuwa yau. Bulkacuwa ita ce ta jagoranci yanke hukuncin shari'ar za~en Gwamnan Jihar Sakkwato a 2007 da kuma na Jihar Bayelsa. Memba a }ungiyar Lauyoyi ta Duniya, Bulkacuwa tana da lambar girma ta OFR, ta kuma fito ne daga Jihar Bauchi bugu da }ari ita ce mace ta farko da ta kafa tarihin zama Shugabar Kotun [aukaka {ara a Nijeriya.

71. Sanata Ibrahim [anbaba Sanata Ibrahim Abdullahi [anbaba shi ne ke wakiltar maza~ar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa ta }asa, ya kuma samu kansa a majalisa ne a za~en shekarar 2015 a }ar}ashin inuwar jam'iyyar APC. Memba ne a kwamitocin Majalisa na aikin soja da sadarwa da wayar da kan al'umma. Sanatan wanda ya kwashe shekaru 35 yana aiki a Gwamnatin Tarayya ya himmatu wajen gudanar da wakilci nagari a can zauren majalisa da kuma maza~arsa wa]anda suka tabbatar da cewar a wakilcinsa ba su yi za~en tumun dare ba.

72. Abubakar Bawa Bwari Hon. Bawa Bwari wanda ya fito sarari a duniyar siyasa a yayin da ya zama Mai Tsawatarwa A Majalisar Wakilai wadda ya kasance memba tun daga 1999 zuwa 2007. Hasali ma a matsayinsa na Bulaliyar Majalisar Wakilai ta Tarayya ya yi amfani da kujerarsa wajen bayar da tashi gudunmuwa ga ci gaban ayyukan majalisa da kuma gudanar da wakilci nagari a maza~arsa ta Suleja/Gurara /Tafa a Jihar Neja. A yau Bawa Bwari shi ne }aramin Ministan Albarkatun }asa, mu}amin da ya ba shi damar fitowa da shiraruwa da dama ta fuskar za}ulowa da ha}o albarkatun }asa da ake da su birjik a wurare da dama wa]anda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata to tattalin arzikin Nijeriya zai }ara ha~aka ya kuma bun}asa.

73. Aliyu Oroji Wamakko Mataimakin Shugaban {ungiyar Masu Sana'ar Gidaje ta Abuja, Oroji Wamakko tsohon jami'in Hukumar Kwastam ne wanda ke taimakawa al'umma a ~angarori da dama. Baya ga fannin samar da muhalli ta hanyar gina gidaje a Birnin Tarayya domin amfanin ma'aikata, 'yan kasuwa da 'yan siyasa, haka ma Oroji a yanzu haka jama'a da dama ne ke cin abinci a }ar}ashin kamfanin sa mai kula da tsaron lafiya da dukiyar al'umma wanda aka fi sani da Je]o Security baya ga Je]o Investment da kuma Khalifa International School wa]anda duka al'umma ke amfana da shi. Ba shakka idan a na samun ire-iren Oroji Wamakko a cikin al'umma to kuwa za a rage wahalar }arancin muhalli tare kuma da bankwana da u}ubar rashin ayyukan yi da musamman matasa a Nijeriya ke fuskanta a Nijeriya.

74. Honarabul Binta Bello Honarabul Binta Maigari Bello ita ce Mataimakiyar Mai Ladabtarwa A ~angaren Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai ta Tarayya. Tana wakiltar maza~ar Kaltungo/Shonam a Jihar Gombe. Gabanin shiga majalisa a shekarar 2011, ta kasance Kwamishinar Lamurran Mata tare da samun kambun Gwarzuwar Kwamishina. Abubuwan da take da ra'ayi sune magance fatara da talauci, bun}asa yankunan karkara da samar da 'yancin cin gashin kai ga }ananan Hukumomi. Haka kuma ayyukan da take son ganin an aiwatar sune aiwatar da ayyukan kasafin ku]i yadda ya kamata, bin diddigin ayyukan ma'aikatu da hukumomin Gwamnati. A kan gudanar da shugabanci nagari, Honarabul Bello ta samu karramawa da digirin girmamawa da kuma karramawa a matsayin Kwamishina mafi }wazo.

75. Ahmad Kuru {wararren ma'aikaci, Ahmad Kuru shi ne Shugaban Kamfanin Kula Da {adarorin Gwamnati wanda aka fi sani da AMCON ya kuma hau mu}amin ne bisa ga cancanta da sanin makamar aiki. Gabanin zama Shugaban AMCON, Kuru shi ne Manajin Darakta na Enterprise Bank Limited ]aya daga cikin bankunan da Babban Bankin Nijeriya CBN ya }ir}iro. Kuru ya jagoranci aiki na }wararru da tabbatar da aminci da yarda tsakanin Bankin da abokan hul]arsa gabanin komawarsa a matsayin Heritage Bank. Kuru ya shiga kamfanin AMCON da }warewa da gogewar aikin banki da hul]ar ku]a]e ta sama da shekaru 35 na aikinsa wa]anda suka samar masa martaba a matsayin jami'i mai }wazo da jagorantar canji. Haka ma Kuru ya taka gagarumar rawa wajen samun nasarar ha]ewar Habib Bank da Platinum Bank a matsayin Bank PHB ]aya daga cikin bankuna mafi iya hul]a da abokan hul]a gabanin komawarsa Keystone Bank.

76. Yakubu Muhammad Gabanin na]a shi a matsayin Shugaban Gidan Talbijin Na {asa NTA, Yakubu Muhammad shi ne Mashawarci na Musamman kan Ya]a Labarai ga Gwamnan Jihar Bauchi. A matsayinsa na wanda ya kwashe tsayin shekaru yana aiki da Gidan Talbijin na NTA tun a matsayin }aramin ma'aikaci zuwa Darakta Janar na NTA baki]aya, ya ]aura ]amarar bun}asa ayyukan hukumar tare da inganta tashar daga tsohon tsari zuwa tafiya daidai da zamani da kuma ya]a }udurori da manufofin Gwamnatin canji.

77. Umaru Ibrahim MNI Alhaji Umaru Ibrahim mni, shi ne Shugaba kuma Babban Jami'in Gudanarwar Hukumar NDIC, mu}amin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ]ora shi a kai. Gabanin samun wannan matsayi ya fara aiki da Hukumar a matsayin Mataimakin Darakta a shekarar 1989 tare da ri}e fannoni da dama gabanin ya zama Darakta Janar a Hukumar a shekarar 2010. Tafiyar da aiki yadda ya kamata tare da gamsuwa da shugabancinsa ne dalilin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ]ora shi saman wannan kujerar a sabon wa'adin shekaru biyar bayan kammala wa'adin farko a watan Disambar shekarar 2015.

78. Isha} Modibbo Kawu Isha} Modibbo Kawu, haifaffen Jihar Kwara a Arewa Ta Tsakiya fitacce ne a duniyar aikin jarida. Shi ne Shugaban Gidan Talbijin Na na farko a Kwara, haka ma ya yi aiki da gidan Radiyon BBC da jaridar Daily Trust a matsayin Edita daga baya kuma Shugaban Kwamitin Editoci. A shekarar 2016 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya na]a shi Shugaban Hukumar Kula Da Kafofin Ya]a Labarai Ta }asa (NBC) tare da alhakin bin diddigi da sanya idanu kan yadda kafafen ya]a labarai ke gudanar da aikin su domin ganin ba su sa~awa }a'idar aiki ba.

79. Mansur Liman Haifaffen Daura a Jihar Katsina, Mansur Liman ya samarwa kansa suna a matsayin nagartaccen ]an jarida a aikin da ya yi da gidan radiyon BBC Hausa a Birnin Landan. Liman wanda ke da digiri na uku na Dakta daga Jami'ar Sussex a Ingila a shekarar 1993 ya samu nasibin gabatar da labarai da zafin su. Shi ne ya bayar da labarin rasuwar Janar Sani Abacha, kuma shi ne ya labartawa duniya rasuwar Cif MKO Abiola. Bugu da }ari tun bayan hawansa karagar mulki shi ne ]an jaridar farko da ya tattauna da Sarkin Kano Ado Bayero. Haka ma Mansur Liman ne ya bayar da labarin tattaunawar Shugaba Jonathan da Muhammadu Buhari inda ya ayyana amincewar fa]uwa za~en a shekarar 2015. Mansur Liman wanda a yau shi ne Shugaban Gidan Radiyon Nijeriya Kaduna (FRCN), ya ]aura ]amarar amfani da }warewa da gogewarsa a aikin ya]a labarai domin ]aga darajar gidan radiyon, kyautata jin da]i da walwalar ma'aikatansa da ya]a kyawawan manufofin Gwamnatin Tarayya.

80. Babangida Ruma Matashi Babangida Ruma, ]an asalin }aramar Hukumar Mulkin Batsari a Jihar Katsina, shi ne Jakadan Zaman Lafiya na Majalisar Matasa ta {asashe Renon Ingila, wata Commonwealth kan fa]akar da jama'a illar ta'addanci a lokacin za~e Shi ne Shugaba kuma wanda ya assasa }ungiyar Arewa Youth Awareness Initiative Forum (AYAIF), kuma Shugaban Ruma Foundation. Babangida Ruma ya yi fice wajen rajin kare hakkin matasa tare da fafatukar ganin matasa sun samu kyakkyawar makoma.

81. Dikko Umar Ra]]a Dikko Umar Ra]]a shi ne Shugaban Cibiyar {anana da Matsakaitan 'Yan Kasuwa ta {asa (SMEDAN) ya kuma hau kujerar ne a shekarar 2016, gabanin zamansa Shugaban wannan Cibiyar shi ne Shugaban Ma'aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina. Tsohon ma'aikacin banki, kuma tsohon shugaban }aramar hukuma, a shugabancinsa ana kyautata tsammanin }anana da matsakaitan 'yan kasuwa za su amfana da shiraruwa da dama na Gwamnatin Tarayya tare da tallafin bashi domin bun}asa sana'o'insu daban-daban.

82. Sulaiman Barau {wararren ma'aikacin Banki, masani hul]ar ku]a]e, Sulaiman Barau shi ne Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya. Ya zama mutum mafi daraja ta biyu a bankin CBN a watan Disamba 2007. Wasu mu}aman da ya ri}e sune Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Babban Bankin Nijeriya da kuma Shugaban Ri}on }warya na Kamfanin Buga Ku]a]e na Nijeriya. Barau yana da ilimi sosai a kan harkar aikin banki da tattalin arziki yana kuma amfani da matsayinsa wajen jagorantar nasarori da dama a Babban Bankin Nijeriya.

83. Dakta Sani H. Aliyu A shekarar da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya na]a Dakta Sani Aliyu a matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Cutar {anjamau ta {asa (NACA) da zummar magance yawaitar masu fama da cutar }anjamau. Dakta Aliyu wanda ya ta~a aiki a matsayin Jami'in Kiwon Lafiya a Asibitin Fadar Shugaban {asa, haka ma ya gudanar da kwasa-kwasai da dama kan sanin makamar aiki a }asashen waje inda ya }ara samun shaidar zama }wararren likita.

84. Ahmed Umar Bolori Sunan Ambasadan zaman lafiya Ahmed Bolori ya fito sarari ne a yayin da Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa jallo a watan Agusta na shekarar 2016 a kan abin da ta ce yana da masaniyar inda 'yan matan Chibok suke tsare a hannun Boko Haram. Daga bisani dai an samu fahimtar juna tsakaninsa da Rundunar Sojin Nijeriya. Bolori ]an shekaru 22 wanda ke fafutukar ganin an samu sulhu tsakanin maya}an Boko Haram da Gwamnati tare da fitowar matan Chibok lafiya }alau ba tare da wata matsala ba, ya jima yana }o}arin wayar da kan al'umma kan muhimmancin zaman lafiya tare da }auracewa tashin-tashina.